An nada Gwamna Shema Sarkin Fulanin Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya nada Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema a sarautar Sarkin Fulanin Katsina na daya a wani kasitaccen biki da aka yi ranar Asabar.A jawabin Sarkin ya nemi gwamnonin kasar nan da shugabannin al’umma su yi koyi da Gwamna Shema wajen jagorancin jama’a bisa adalci da […]
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya nada Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema a sarautar Sarkin Fulanin Katsina na daya a wani kasitaccen biki da aka yi ranar Asabar.
A jawabin Sarkin ya nemi gwamnonin kasar nan da shugabannin al’umma su yi koyi da Gwamna Shema wajen jagorancin jama’a bisa adalci da sanin ya kamata ta yadda ci gaba zai samu ga al’umma.
Ya ce Jihar Katsina ta kasance abar misali ta fuskar ci gaba a matakai daban-daban da kowa ke gani a yau, wannan ya sa Masarautar Katsina ta ga dacewar ta ba shi sarautar Sarkin Fulanin Katsina na daya.
Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce Gwamna Ibrahin Shema ya samar da kyakkyawan ci gaba a jihar a fannin ba da ilimi kyauta da shirin bunkasa noma inda ya ba da misali da shirin nan na Shanghai da horar da matasa sana’o’i.
A wani labarin Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo ya yaba wa Gwamna Ibrahim Shehu Shema bisa kammala aikin ginin sakatariyar Jam’iyyar PDP ta jihar.
Alhaji Namadi Sambo ya yi wannan yabo ne lokacin da yake bude sakatariyar inda ya bukaci gwamnonin PDP su yi koyi da irin rawar da Gwamna Shema ya taka don ganin an samu irin wannan tsari a jihohinsu.
A jawabin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya nuna jin dadi bisa samu sakatariyar jam’iyyar da take da yanayi mai kyau na gudanar da ayyuka.
Sannan ya ce zai jagoranci Jam’iyyar PDP bisa adalci da sanin ya kamata domin ganin an cimma nasarar da ake bukata, inda ya sha alwashin ganin dukkan wadanda suka bar jam’iyyar sun dawo cikinta da yardar Allah. Gwamnonin PDP 10 ne suka halarci wannan bikin, wanda a bayansa suka gudanar da taron gwamnonin PDP.