An nada Hauwa Idris Zinariyar Yamaltu
A ranar Asabar Mai martaba Sarkin Yamaltu da ke Jihar Gombe Alhaji Hassan Usman Jonga ya nada Hajiya Hauwa Idris Umar sarautar Zinariyar Yamaltu.An yi bikin nadin ne a fadar mai martaba Sarkin Yamaltu, inda bikin ya samu halarta dimbin jama’a daga ciki da wajen kasar nan.Hajiya Hauwa Idris matar Ministan Sufuri ta bayyana farin […]
A ranar Asabar Mai martaba Sarkin Yamaltu da ke Jihar Gombe Alhaji Hassan Usman Jonga ya nada Hajiya Hauwa Idris Umar sarautar Zinariyar Yamaltu.
An yi bikin nadin ne a fadar mai martaba Sarkin Yamaltu, inda bikin ya samu halarta dimbin jama’a daga ciki da wajen kasar nan.
Hajiya Hauwa Idris matar Ministan Sufuri ta bayyana farin cikinta da kuma godiya ga Sarkin Yamaltu sakamakon nada ta sarautar Zinariyar Yamaltu da ya yi.
Ta ce “Ba zan iya bayyana farin cikin da nake ciki ba, musamman dangane da kwarin gwiwar da masarautar Yamaltu take da shi a kaina, har ta nada ni sarauta, musamman shaidar da aka yi mini ta cewa ina taimakon al’umma.” Inji ta.
Bayan ta kammala jawabi ne aka gudanar da hawan daba a kofar fadar Sarkin Yamaltu.
Bayan an kammala hawan daba ne Hajiya Hauwa ta kaddamar da wata cibiya da za ta rika taimaka wa matasa ta hanyar koya musu sana’o’in don su dogara da kansu.
Kwamishinar Mata ta Jihar Gombe Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad ce ta wakilci matar gwamnan Jihar Gombe, wadda ta bude cibiyar a kauyen Hinna da ke kusa da garin Yamaltu.
Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Sani Musa Danja ne ya nishadantar da taron.
A cikin wadanda suka halarci bikin akwai Hajiya Falmata Mohammed Wakil matar karamin Ministan Wutar lantarki da Hajiya Sa’adatu Bashir Yuguda matar karamin Ministan Kudi da Hajiya Hananiya da Hajiya Umma Umar Faruk da Hajiya Fati Yalo da sauransu.