An nada Kutigi Shugaban Taron kasa
Shugaba Goodluck Jonathan ya nada tsohon Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Idris Kutigi a matsayin Shugaban Babban Taron kasa da za a yi nan ba da dadewa ba. Wata sanarwa da ta fito daga Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim ta ce an kuma nada tsohon Ministan Harkokin kasashen Waje Farfesa Bolaji Akinyemi a matsayin […]
Shugaba Goodluck Jonathan ya nada tsohon Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Idris Kutigi a matsayin Shugaban Babban Taron kasa da za a yi nan ba da dadewa ba.
Wata sanarwa da ta fito daga Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim ta ce an kuma nada tsohon Ministan Harkokin kasashen Waje Farfesa Bolaji Akinyemi a matsayin Mataimakin Shugaban Babban Taron yayin da aka nada Dokta balerie Azinge ta zama Sakatariyar Babban Taron.
Sanarwar ta ce shugabannin Babban Taron za su fara aiki ne a shekarajiya Laraba a Abuja, yayin da ake sa ran fara taron a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda Shugaba Jonathan ya fada a makon jiya.
Gwamnatin Tarayya ta ce wakilai 492 ne za su halarci taron wanda ta ce za a shafe wata uku ana musayar ra’ayoyi a kan batutuwan da suka shafi kasar, amma ba za a tabo batun raba kasa a ciki ba.
Ta kuma ce bayan an kammala taron mahalarta taron za su ba da shawarwari a kan matakan da Gwamnati Tarayya ya kamata ta dauka domin zartar da abubuwan da aka cimma su zama doka.
Sai dai Puis Anyim ya ce idan ba a cimma daidaito ba a kan abubuwan da aka zartar a taron, za a yarda da abubuwan da kashi 75 cikin 100 na mahalarta taron suka amince da su.
Mai shari’a Kutugi wanda dan Jihar Neja an haife sh ne a ranar 31 ga Disamban 1939, kuma ya zama Babban Jojin Najeriya daga 30 ga Janairun 2007 zuwa Disamban 2009.
Ya halarci makarantun shari’a a Najeriya da Ingila, kuma ya taba zama Kwamishinan Shari’a na Jihar Neja kafin ya zama alkalin Babban Kotu a 1976. Ya zama alkali a Kotun koli a 1992 inda ya shekara 10 kafin ya zama shugabanta.
Shi kuwa Farfesa Akinyemi ya fito ne daga Ilesa a Jihar Osun kuma ya samu iliminsa a Najeriya da Ingila da Amurka tare da gudanar da ayyuka da dama kafin Janar Babangida ya nada shi Ministan Harkokin Waje a 1985.
Ita kuwa Dokta Azinge wadda ta fito daga Jihar Enugu ta yi digirnta kan shari’a ne a Jami’ar Jos a 1984, kafin ta zarce Ingila don digirinta na biyu, sannan ta yi digiri na uku a Jami’a Ambrose Alli da ke Jihar Edo. Fitacciyar lauya ta taba zama wakiliya a Hukumar Gudanarwa ta Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa.