An nada mace shugabanci a masallacin Ka’aba
A ranar Litinin da ta gabata ne aka nada Malama Fatimah al-Rashoud akan mukamin shugabanci a manyan masallatai biyu masu alfarma wato masallacin Makkah da Madinah , kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.Shugaban Gudanarwar Masallatan Sheikh Abdulrahman al-Sudais ya bayyana cewa an bai wa matar shugabancin Kwamitin Shiryar da Al’umma da kuma kula da […]
A ranar Litinin da ta gabata ne aka nada Malama Fatimah al-Rashoud akan mukamin shugabanci a manyan masallatai biyu masu alfarma wato masallacin Makkah da Madinah , kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Shugaban Gudanarwar Masallatan Sheikh Abdulrahman al-Sudais ya bayyana cewa an bai wa matar shugabancin Kwamitin Shiryar da Al’umma da kuma kula da dakunan karatun masallatan. Kuma an dauki wannan matakin ne saboda irin gudunmuwar da mata suke bayar wa wajen ci gaban masallatan da kuma yadda ake kiraye-kirayen shugabancin mata a aikace-aikacen gudanarwar masarautar kasar. Kodayake, tun a bara ne Sheikh al-Sudais ya nada al-Rashoud a matsayin mataimakiyar shugaban kwamitin. Ya ci gaba da cewa an yi amannar cewa mata sun fi maza cancantar bai wa takwarorinsu mata shawara kan shiriya bisa turbar addini.
Ya kara da cewa: “Ba sa mantawa bukatocinsu da halin da suke ciki. Masarautar kasar kanta ta nada kwararrun mata malaman addini wadanda suke ba da darussa a masallatai.”
A nata bangaren Malama al-Rashoud ta bayyana nadin da wata dama da za ta kara mata jajircewa da sadaukar da kai da kuma karfafa mata gwiwa wajen aikinta. “Ina cikin matukar annashuwa saboda nada ni a matsayin wadda za ta kula da duk wata macen da za ta ziyarci wadannan masallatai masu alfarma, ” inji ta.