An nada sabon babban limamin Ibadan

Al’ummar Musulmi a birnin Ibadan suna ci gaba da zaman makokin rasuwar babban Limamin Ibadan, Sheikh Busari Suara Haruna, wanda ya rasu da Asubahin ranar Alhamis ta makon jiya. A wannan rana ce aka yi masa jana’iza da binne gawarsa a harabar gidansa da ke unguwar Agbeni cikin birnin Ibadan.Marigayi Sheikh Busari Suara Haruna mai […]

An nada sabon babban limamin Ibadan
An nada sabon babban limamin Ibadan

Al’ummar Musulmi a birnin Ibadan suna ci gaba da zaman makokin rasuwar babban Limamin Ibadan, Sheikh Busari Suara Haruna, wanda ya rasu da Asubahin ranar Alhamis ta makon jiya.

A wannan rana ce aka yi masa jana’iza da binne gawarsa a harabar gidansa da ke unguwar Agbeni cikin birnin Ibadan.
Marigayi Sheikh Busari Suara Haruna mai shekaru 93 ya rasu ne bayan wata gajeruwar rashin lafiya. Kafin rasuwarsa shi ne yake rike da mukamin babban Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na jihohin Kudu maso yamma. Mataimakinsa babban limamin Ado Ekiti, Sheikh Jami’u Kehulere shi ne ya jagoranci dimbin Musulmi wajen yi masa Sallar jana’iza da aka yi a harabar babban masallacin Ibadan. Marigayin ya rike wannan matsayi na tsawon shekaru 20.
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi yana daga cikin manyan mutane da suka halarci wajen jana’izar. Shi ma dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Otunba Christopher Adebayo Alao Akala, ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan marigayin a wannan rana.
A lokacin yana raye Sheikh Busari Haruna, ya yi suna wajen yin wa’azi musamman ga attajiran Musulmi masu hannu da shuni da manyan ’yan siyasa da su ji tsoron Allah (SWT) kuma su yi amfani da dukiyarsu wajen gina addininsu kuma su yi adalci ga harkokin siyasa.
Wa’azin da ya yi na karshe kafin rasuwarsa ya yi ne a lokacin da aka yi jana’izar hamshakin dan kasuwan nan na Ibadan, Alhaji Muftahu Olanihun mako biyu da wucewa, a inda marigayin ya tunatar da al’ummar Musulmi a game da amfanin shimfida kyawawan abubuwa a duniya domin samun rahamar Ubangiji a gobe kiyama.
A shekaranjiya Laraba ne babban kwamitin al’ummar Musulmi na Ibadan da hadin gwiwar majalisar limaman Ibadan suka bayar da sanarwar nada Sheikh Alhaji Abdul-Ganiyy Abubakari Agbotomokekere, mai shekaru 80 a matsayin sabon limamin Ibadan na 18.
Da yake bayar da sanarwar nada sabon limamin a wajen taro da ’yan jarida a zauren taro na babban masallacin Ibadan Shugaban kwamitin Musulmin Ibadan Alhaji Mustapha Bayo Oyero ya ce, dukkan masu ruwa da tsaki a al’amuran Musulmin Ibadan sun nuna amincewarsu dari bisa dari na nadin sabon babban limamin da kwamitin limamai ya bayar da sunansa tun farko.
Haka kuma, a jiya Alhamis, dubunan Musulmi maza da mata suka yi cincirindo a cikin filin wasanni na Lekan Salami da ke Adamasingba a Ibadan domin yin addu’ar Fidda’u ta kwana 7 da rasuwar limamin Ibadan Sheikh Busari Suara Haruna. Kuma a wajen wannan addu’o’i ne aka tabbatar da nada Sheikh Abdu-Ganiyy Abubakari Agbotomokekere a matsayin sabon limamin na Ibadan da aka nada masa rawani da sanya masa Alkyabba tare da mika masa wata sanda, domin tabbatar da nadin nasa ga duniya. Shugabannin Musulmi daga sassa daban-daban na kasa ne suka halarci wajen wannan addu’a.