An nada sabon Dagacin Kachi

Masarautar Dutse a Jihar Jigawa ta tabbatar da nadin Alhaji Haruna danbaba a matsayin Dagacin Kachi da ke yankin Kiyawa bayan tsige tsohon Dagaci Malam Shafi’u Abdullahi sakamakon zarginsa da yin lalata da wata mace, lamarin ya kai aka a yi masa tsirara a bainar jama’a a garin Kiyawa da ke karamar Hukumar Kiyawa kimanin […]

An nada sabon Dagacin Kachi
An nada sabon Dagacin Kachi

Masarautar Dutse a Jihar Jigawa ta tabbatar da nadin Alhaji Haruna danbaba a matsayin Dagacin Kachi da ke yankin Kiyawa bayan tsige tsohon Dagaci Malam Shafi’u Abdullahi sakamakon zarginsa da yin lalata da wata mace, lamarin ya kai aka a yi masa tsirara a bainar jama’a a garin Kiyawa da ke karamar Hukumar Kiyawa kimanin wata uku da suka gabata, bayan matasa sun yi garkuwa da shi.

Sakamakon zubar wa masarautar da mutunci da tsohon Dagacin ya yi ne Masarautar Dutse ta tsige shi ta kuma tabbatar da nadin Malam Haruna danbaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Hakimin Birnin Dutse Alhaji Jamilu Turaki ya ce zaben Dagacin na Kachi ya biyo bayan sauke tsohon Dagacin ne saboda samunsa da masarauta ta yi da aikata wasu manyan laifuffuka da take ganin ba za ta amince masu irin wannan hali su kasance jagororin jama’a ba.
Alhaji Jamilu ya hori jama’ar yankin Kachi su bai wa sabon Dagacin hadin kai domin ciyar da yankin gaba, inda ya ce nan ba da dadewa ba za a shirya biki a fadar Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi don nada sabon Dagacin.
Ya hori sabon Dagacin ya rike gaskiya ya guji aikata abin da zai zubar da mutuncinsa ya zubar da mutuncin masarautar.
Wakilimmu na Dutse ya zanta da sabon Dagacin inda ya gode wa masarautar Dutse kan nada shi a kan wannan sarauta kuma ya yi alkawarin tafiya tare da jama’arsa, inda ya yi kira ga mutanen gidan da sarautar ta fita daga hannunsu su zo su hada hannu da shi domin ciyar da yankin gaba.