An nada sabon Darakta Janal na NYSC

Rundunar sojin saman Najeriya, ta amince da wasu sabbin nade-nade da kuma sauyin wurin aiki, ga manyan sojin kasar. A wata sanarwa da aka fitar yau Juma’a da kakakin rundunar sojin, Kanal Sagir Musa ya sanar na cewa, wadanda al’amarin ya shafa har da Manjo Janal S Z Kazaure, wanda shi ne babban daraktan Shirin […]

An nada sabon Darakta Janal na NYSC

Rundunar sojin saman Najeriya, ta amince da wasu sabbin nade-nade da kuma sauyin wurin aiki, ga manyan sojin kasar.

A wata sanarwa da aka fitar yau Juma’a da kakakin rundunar sojin, Kanal Sagir Musa ya sanar na cewa, wadanda al’amarin ya shafa har da Manjo Janal S Z Kazaure, wanda shi ne babban daraktan Shirin Yiwa Kasa Hidima, NYSC, yanzu an mayar da shi cibiyar kula da tattara bayanan sojoji, a matsayin babban jami’i a cibiyar.