An nada sabon Daraktan Hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya nada Alhaji Suleiman Nuhu Kuki a matsayin sabon Daraktan hukumar jin dadin alhazai na Jahar. An nada Alhaji Suleiman, ne bayan rushe jagororin hukumar da Gwamnan ya yi a kwanakin baya bisa zargin su da yin almundaha da ha’intar gwamnatin gami da gazawarsu ta rike amanar da […]

An nada sabon Daraktan Hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya nada Alhaji Suleiman Nuhu Kuki a matsayin sabon Daraktan hukumar jin dadin alhazai na Jahar.

An nada Alhaji Suleiman, ne bayan rushe jagororin hukumar da Gwamnan ya yi a kwanakin baya bisa zargin su da yin almundaha da ha’intar gwamnatin gami da gazawarsu ta rike amanar da aka ba su.

Wanda hakan ya yi sanadiyar har wasu maniyatan aikin hajjin 2019 su 150 suka rasa masaukin su a garin Makka duk kuwa da cewa, babu wani maniyacin da ake zaton zai samu wata matsala ta irin yadda gwamnatin tayi kokarin bayar da duk wasu abubuwan da ake bukata.

Kafin nadin na shi, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya taba rike hukumar bayar da ilmin bai daya wato SUBEB, daga nan ya zama mai bai wa Gwamna shawara akan hukumar ilmin kimiya da fasaha a lokacin gwamnatin Shema ta PDP.

Bayan canjin gwamnati, Kuki ya dawo a matsayin Daraktan sashen kudi da mulki a ma’aikatar ilmi ta Jaha.

Alhaji Suleiman ya samu canjin wajen aiki zuwa Ma’aikatar aiyuka har ila yau a bisa wannan mukami na DAS. Yana kan wannan kujerar ce, a yanzu Gwamna Masari ya bashi Babban Daraktan a ita hukumar jindadin alhazan na Jaha.

Sabon Daraktan ya nuna farin cikinsa akan wannan matsayi da Allah ya ba shi inda ya yi alkawarin rike amana tare da yin aiki tukuru gami da neman hadin kan su ma’aikatan hukumar da zasu yi aiki tare.