An nada sabon Firaminista a Burkina Faso
Mahukunta a kasar Burkina Faso sun nada Laftanar Kanar Isaac Zida a matsayin firaministan gwamnatin rikon kwarya. Kanar Zida yana daya daga cikin sojojin da suka karbe iko lokacin da Shugaba Blaise Compaore ya yi murabus ranar 31 ga watan jiya bayan wata zanga-zangar gama gari da ta tilasta masa yin hakan.Da fari kanar din […]
Mahukunta a kasar Burkina Faso sun nada Laftanar Kanar Isaac Zida a matsayin firaministan gwamnatin rikon kwarya.
Kanar Zida yana daya daga cikin sojojin da suka karbe iko lokacin da Shugaba Blaise Compaore ya yi murabus ranar 31 ga watan jiya bayan wata zanga-zangar gama gari da ta tilasta masa yin hakan.
Da fari kanar din ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, amma a ranar Talata bayan cimma wata yarjejeniya wadda cikinta za a gudanar da zabubbuka nan da shekara guda, an nada sabon shugaban wato tsohon Ministar Harkokin Wajen kasar Michel Kafando a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.
Yarjejeniyar ta bai wa sabon shugaban karfin iko, wanda shi ne mutumin da sojojin kasar suka mika sunansa. Kuma yarjejeniyar ta bukaci kafa majalisar dokokin wucin gadi wadda za ta yi aiki har zuwa badi.
Ana sa ran cewa KanarZida zai yi taron tattaunawa kan kafa gwamnatin rikon kwarya. Kodayake, kanar din yana daya daga cikin dakarun da suka yi aiki fadar tsohon Shugaban kasa Compaore.
Mista Compaore ya karbi mulki ne a shekarar 1987 ta hanyar juyin mulki. Kuma ya ci gaba da mulkin kasar ta hanyar lashe zabe har sau hudu. Sai dai a cikin watan jiya ne jama’a suka fantsama titunan babban birnin kasar, Ouagadougou don bayyana adawarsu ga kara neman wa’adin mulki da shugaban ya bukata daga gare su.