An nada sabon Firaminista a Faransa
Gwamnatin Faransa ta nada Ministan Harkokin Cikin Gida, Bernard Cazeneuve a matsayin sabon Firaministan kasar bayan Manuel Valls ya yi murabus daga wannan mukamin a ranar Talata. Mista Valls ya ajiye aikinsa ne tare da amincewar shugaba Francois Hollande bayan ya sanar da aniyyarsa ta tsayawa takara a zaven shugabancin kasar mai zuwa a karkashin […]
Gwamnatin Faransa ta nada Ministan Harkokin Cikin Gida, Bernard Cazeneuve a matsayin sabon Firaministan kasar bayan Manuel Valls ya yi murabus daga wannan mukamin a ranar Talata.
Mista Valls ya ajiye aikinsa ne tare da amincewar shugaba Francois Hollande bayan ya sanar da aniyyarsa ta tsayawa takara a zaven shugabancin kasar mai zuwa a karkashin inuwar jam’iyyar gurguzu.
A cewar tsohon firaministan, ba ya fatan Faransa ta fada a hannun masu ra’ayin rikau, kamar dai yadda hakan ya kusa faruwa a shekarar 2002, saboda haka zai gudanar da yakin neman zave tare da kara nuna rashin amincewa da dan takarar adawa da kuma manufofinsa, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI ta bayyana.
“Wannan dan takara ne da ba shi da manufofi face irin wadanda aka aiwatar a shekarun 1980, wadanda kowa ya tabbatar ba abin da suka haifar wa kasa face koma-baya,” inji Manuel Valls.
Mista Valls ya kara da cewa, babban aikinsa a yau shi ne, sake hada kan magoya bayan jam’iyyarsu ta Socialist mai mulkin Faransa.