An nada sabon Firayiministan Masar
Tsohon Ministan gidaje na kasar Masar, Ibrahim Mahlab shi aka nada a amtsayin sabon Firayiministan kasar, bayan da Gwamnatin da sojoji suka kafa bayan sun hambarar da shugaba Muhammad Mursi, a karkashin jagorancin Beblawi ta yi murabus. Wannan Firayiministan wani jigo ne a hambararriya gwamnatin Shugaba Husni Mubarak, wadda guguwar juyin juya halin kasashen Larabawa […]
Ibrahim Mahlab, newly appointed minister of housing of Egypt’s interim cabinet which was formed on July 16, 2013, speaks to the media at his office in Cairo in this picture taken on July 1, 2010. Thousands of supporters of deposed Egyptian President Mohamed Mursi demonstrated outside the prime minister’s office on July 17, 2013 in […]

Tsohon Ministan gidaje na kasar Masar, Ibrahim Mahlab shi aka nada a amtsayin sabon Firayiministan kasar, bayan da Gwamnatin da sojoji suka kafa bayan sun hambarar da shugaba Muhammad Mursi, a karkashin jagorancin Beblawi ta yi murabus. Wannan Firayiministan wani jigo ne a hambararriya gwamnatin Shugaba Husni Mubarak, wadda guguwar juyin juya halin kasashen Larabawa ta yi awomn gaba da ita.
A wata sanarwa da ya bayar a taron ’yan jarida, bayan an nada shi, Mahlab ya ce zai majalisar mulkin “mayaka,” wada za ta yi wa Misirawa hidima, don tabbatar da tsaro a kasar, a matsayin al’amarin da za ta fi bai wa fifiko.
“Za mu yi aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro a Masar da kuma kawar da ta’addanci a kowane sako na kasar nan,” inji shi.
Mahlab, tsohon jami’in hambararriyar Gwamnati Hosni Mubarak ne, kuma dan Jam’iyyar NDP, sghi injiniyan gine-gine ne, da ya taba jagorantar Kamfanin gine-gine na Arab Contractors,” wadda ya zamanto babban kamfanin gine-gine a kasar Masar.
An nada shi a matsayin sabon Firayiministan ne bayan da Hazem Bablawi ya mika takardar murabus din gwamantinsa. Wannan shiri dai masu sharhi kan harkokin siyasar kasar na ganinsa, tamkar sharar fage ne ga shugaban rundunar Sojan kasar, kuma Ministan tsaro, Abdel-Fattah el-Sissi, don tsayawa takarar shugazbancin kasar, ta yadda za a shawo kan bacin ran al’umma wajen nuna gazawar da gwamantin ta yi na farfado da tattalin arikin kasar, da inganta ayyukan gwamnati.