An nada sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Tarayya
Majalisar ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin.
Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai.
Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin.
Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata.
A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu sun fito ne daga Jihar Ogun.