An nada sabon Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya nada Malam Junaid Mahmud a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

An nada sabon Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau

Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau Alhaji Janairu Mahmud

Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya nada Malam Junaid Mahmud a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

Malam Junaid dai ya fito ne daga gidan Sarautar Bare-bari, kuma mahaifinsa, Malam Mahmud da ne ga Marigayi Madakin Zazzau Shehu wanda shi kuma Da ne ga Sarkin Zazzau Dalhatu.

Malam Junaid ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya kuma ya yi aiki da Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) inda ya rike mukamin Babban Jami’in Gudanarwa har zuwa lokacin da ya kammala aikin sa.

Sabon Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau dai ya gaji Marigayi Alhaji Ibrahim Shehu Idris ne, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a makon da ya gabata.