An nada sabon Sarkin Hausawan Ajegunle
Sarkin Hausawan Jihar Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara, ya nada Alhaji Ummaru Sidi a matsayin sabon sarkin Hausawan yankin Ajegunle. Nadin wanda aka yi a kofar fadar sarkin da ke unguwar Ajegunle a karshen makon da ya gabata, ya samu halartar sarkin Fulanin Legas, Alhaji Abubakar Muhammadu Bambado da sauran sarakunan Hausawa da na Yarabawa […]
Sarkin Hausawan Jihar Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara, ya nada Alhaji Ummaru Sidi a matsayin sabon sarkin Hausawan yankin Ajegunle.
Nadin wanda aka yi a kofar fadar sarkin da ke unguwar Ajegunle a karshen makon da ya gabata, ya samu halartar sarkin Fulanin Legas, Alhaji Abubakar Muhammadu Bambado da sauran sarakunan Hausawa da na Yarabawa da sauran kabilun da ke jihar.
Da yake jawabi jim kadan bayan nadin sabon sarkin, Sarkin Hausawan Legas, ya ce: “Mun nada sarkin ne ba don komai ba sai don saboda cancantar da ya yi da kuma gadon sarautar da ya yi daga mahaifinsa marigayi Malam Sidi. Babu shakka wannan sarauta gidansu ne suke yin ta tun fil azal kuma mahaifinsu shi ne wanda yake sarautar yankin Ajegunle har zuwa Badagiri a shekaru masu yawa da suka wuce. Don haka wannan nadi da muka yi ya dace kuma mun yi shi bisa ka’ida da tsari.”
Sarki Aminu ya taya sarkin murna kuma ya bukace shi ya yi adalci a tsakanin al’umma.
A jawabinsa, sabon sarkin na Ajegunle da aka nada, ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki sannan kuma ya gode wa sarki Aminu tare da ’yan majalisarsa da kuma sarkin Fulani, Alhaji Bambado.
Sabon sarkin ya lashi takobin sauke nauyin da Allah Ya dora masa tare da yin adalci ga jama’a.
Ya yi alkarin cewa zai yi kokari wajen ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin Hausawa da sauran kabilun Jihar Legas.
“Babu shakka wannan babban nauyi ne aka dora mani amma ina mai ba da tabbacin cewa zan gudanar da adalci tare da tabbatar da zaman lafiya. Ina godiya ga Sarkin Hausawa, Alhaji Aminu Yaro Dogara da Sarkin Fulani da sauran sarakunan Jihar Legas da kuma jama’ar Ajegunle da sauran mutanen da suka taimaka wajen ganin wannan abu ya tabbata.” In shi.