An nada sabon sarkin Hausawan Apata NNPC a Ibadan

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya tabbatar da nadin Alhaji Sahabi Sulaiman a matsayin sabon Sarkin Hausawan kauyen Apata kusa da matattarar mai ta NNPC da ke Ibadan, kuma ya yi masa fatan zai rike mukamin cikin amana da adalci. Sabon Sarkin Hausawan, wanda yake cikin kungiyar Abule, masu sana’ar hakar yashi da […]

An nada sabon sarkin Hausawan Apata NNPC a Ibadan

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya tabbatar da nadin Alhaji Sahabi Sulaiman a matsayin sabon Sarkin Hausawan kauyen Apata kusa da matattarar mai ta NNPC da ke Ibadan, kuma ya yi masa fatan zai rike mukamin cikin amana da adalci.
Sabon Sarkin Hausawan, wanda yake cikin kungiyar Abule, masu sana’ar hakar yashi da duwatsu domin sayarwa, ya gaji marigayi Alhaji Abdu Abdullahi ne, wanda ya rasu watanni biyu da suka wuce.
daruruwan jama’a da suka hada da al’ummar Hausawa da dattijan Yarbawa masu sana’a iri daya da sabon sarkin, sanye da sutura iri daya, suka yi jerin gwano da kade-kade da busar algaita daga Apata zuwa unguwar Sabo, inda aka tabbatar da nadin.                                    
Dattijan gari  kamar Magajin Gari, Alhaji Garba Leku da Wali, Alhaji Abdu Mashal da Sarkin Dawaki, Alhaji Umba Bawa da Sarkin Malamai, Sheikh Musa Ali dambaba da kuma Limamin babban masallacin Sabo, Sheikh Rufa’i Husaini duk sun halarci bikin nadin.
Da yake zantawa da Aminiya, a wajen liyafa a gidansa da ke unguwar Bako a kauyen na Apata, sabon sarkin ya yi godiya ga Allah da neman taimakonSa kan matsayin jagorancin jama’a, wanda bai taba tunanin kaiwa gare shi ba, ya yi fatan alheri ga ’yan uwansa Hausawa da Yarbawa da suka dage wajen ganin an nada shi a matsayin shugabansu.Ya kuma bukaci ci gaba da samun hadin kai da goyon bayan jama’a, “Dangane da wannan babban aiki da ke gabanmu, na rike amana, musamman domin tabbatar da zama lafiya tsakanin jama’ata da mutanen gari”.
Dangane sana’arsa kuwa, sarki Sahabi ya ce shekaru 43 suna tare da, “Wadannan Yarabawa, tun muna koyon aiki har muka kawo yanzu, mun zama kamar uwa daya uba daya, ba zan yi watsi da sana’ata ba,  amma ina tabbatar da za mu saurari koke-koken jama’a kuma mu samo hanyar magance matsalolinsu. Saukin hanyar sadarwa ya sa na  bayar da lambata ga jama’a don tuntuba”.
A karshe ya nemi jama’arsa su kasance masu hakuri, musamman wajen kyautata mu’amala a tsakaninsu da jama’ar gari, kuma masu girmama doka da oda.