An nada sabon Sarkin Musulmin Yarbawa

Majalisar Limamai da Malamai (League of Imams and Alfas) a Jihohin Kudu maso Yamma da Edo da Delta, ta tabbatar da nadin Alhaji Dawud Makanjuola Akinola a matsayin sabon Aare Musulmi na kasar Yarbawa da zai maye gurbin marigayi Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, wanda ya rasu shekara daya da ta wuce. Wakilan […]

An nada sabon Sarkin Musulmin Yarbawa
An nada sabon Sarkin Musulmin Yarbawa

Majalisar Limamai da Malamai (League of Imams and Alfas) a Jihohin Kudu maso Yamma da Edo da Delta, ta tabbatar da nadin Alhaji Dawud Makanjuola Akinola a matsayin sabon Aare Musulmi na kasar Yarbawa da zai maye gurbin marigayi Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, wanda ya rasu shekara daya da ta wuce. Wakilan Majalisar daga Jihohin Legas da Ogun da Oyo da Osun da Ondo da Ekiti da Edo da Delta su ne suka tabbatar da nadin ne a wajen taron yini daya da suka yi a Ibadan a ranar Litinin.
Sakataren Majalisar na kasa, Babban Limamin garin Owo a Jihar Ondo, Sheikh Ahmad Olagoke Aladesawe, shi ne ya gabatar da sabon Aare Musulmi ga Shugaban Majalisar na kasa, Limamin Ibadan, Sheikh Jami’u Bello Keulere, wanda ya sanya masa albarka da neman ya tashi tsaye wajen nuna tsoron Allah (SWT) da yin adalci ga dukkan al’amuran da suka shafi al’ummar Musulmi a matsayinsa na sabon Jagora a wannan sashe.
Cikin jawabin amincewa da nadin da aka yi masa, sabon Sarkin Musulmi na kasar Yarbawa, Aare Musulmi, Alhaji Dawud Makanjuola Akinola, ya nuna farin cikinsa da nadin da aka yi masa wanda yace “ban taba tunanin za a zabe ni a matsayin Aare Musulmi na kasar Yarbawa ba domin ina ganin ban yi abubuwan da za su iya kai ni ga wannan matsayi ba. Amma na ga bai kamata na ki amincewa da wannan kira da aka yi mani domin bauta wa Ubangiji (TWT) ba, musamman domin wannan wata dama ce da za ta karfafa mani gwiwar kara bayar da gudunmawa ta ga jama’a da ci gaban addinin Musulunci.
“Na amince da wannan nadi da aka yi mani a matsayin sabon Aare Musulmi na kasar Yarbawa, amma ina neman ku taimaka mani da addu’a da goyon baya a kowane lokaci domin sauke wannan nauyi. Marigayi Aare Musulmi na kasar Yarbawa Alhaji Abdul Azeez Arisekola, shi ne ya aza wannan tubali da nake rokon dukkan Musulmi a wannan sashe su taimaka mani wajen karasa aikin ginawa, domin amfanin Musulmi a Najeriya da duniya baki daya”  inji Sabon Sarkin Musulmin.
 A wani bincike da Wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, akwai wasu fitattun kungiyoyin Musulmi kamar Muslim Ummah of South West Nigeria (MUSWEN) da National Council of Muslim Youth Organasation (NACOMYO) da Muslim Community of Oyo State (MUSCOYS) da wasu manyan mutane masu fada aji maza da mata da ba su halarci wajen taron da Majalisar Limamai da Malaman tayi a Ibadan ba. Wata majiya mai tushe ta shaida wa Wakilinmu cewa, “rashin gayyatarmu ne ya hana mu zuwa wajen wannan taro na Ibadan, domin majalisar limaman ba ta bi tsarin da ya dace wajen nada sabon Aare Musulmi ba.