An nada sabon Shugaban Hukumar Alhazan Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya nada Malam Salihu S. Abubakar a matsayin sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar
Malam Salihu S. Abubakar ya zama sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna.
Gwamna Uba Sani ya nada Malam Salih ya zama sabon sbugaban hukumar ne bayan ya sallami Sakataren Dokta Yusuf Yakubu Arigasiyyu daga mukamin.
Gwamnan ya kuma nada Arrigasiya a matsayin sabon Manajan Daraktan Hukumar Kula Tsaftar Muhalli ta jihar (KEPA).
A daren Lahadi ne kakakin gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya sanar da nadin sabon shugaban hukumar.
- Kisan ’Yan Mauludi: Sanatoci sun ba da gudummawar N109m
- Mutum 16 sun mutu 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna
Ya ce gwamnan na fatan sabon shugaban hukumar alhazan zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin 2024 cikin nasara.
Sanarwar ta ce sabon shugaban hukumar zai kasance yana da duk ikon ofishin tsohon sakataren hukumar.
Ya kara da cewa sakataren kwamiti na musamman na aikin Hajjin 2024 na hukumar, zai kasance sakataren gudanarwan hukumar.