An nada sabon Shugaban Hukumar zabe ta kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, inda ya tabbatar da nadin Farfesa Mahmud Yakubu. Majalisar mulkin kasa ta tabbatar da nadin a wani taron gaggawa da ta gudanar a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.Taron shi ne na farko da Shugaba Buhari ya jagoranta.Baya ga nada Shugaban hukujar zaben, […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, inda ya tabbatar da nadin Farfesa Mahmud Yakubu.
Majalisar mulkin kasa ta tabbatar da nadin a wani taron gaggawa da ta gudanar a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Taron shi ne na farko da Shugaba Buhari ya jagoranta.
Baya ga nada Shugaban hukujar zaben, majalisar ta amince da nadin sababbuin kwamishinonin zabe biyar, wadanda suka hada da Amina Zakari a Yankin Arewa maso Yamma; da Anthonia Okoosi-Simbine ta Arewa ta tsakiya da baba Shettima Arfo a yankin Arewa maso Gabas. Sauran kuwa sun hada da Soyebi Adedeji Solomon na yankin Kudu maso Yamma da Mohammed Mustafa Lecky na Kudu maso Kudu.
Misis Zakari, wadda yadda yanzu ta zama kwamishinar hukumar ta kasa, ta rike shugabancin hukumar na wucin gadi, tun daga 30 ga yunin bana, bayan da wa’adin aikin Farfesa Attahitu Jegta ya cika.
Shi kuwa sabon Shugaban Hukunmar, Farfesa Muhammad Yakubu, kwararren masanin tarihi ne da harkokin duniya, sannan ya kasance Babban Sakataren Asusun Raya Manyan makarantu. Ya kuma halarci taron kasa da aka gudanar a shekarar 2014.