An nada Saraki Daraktan yakin neman zaben Atiku

A ranar Talatar da ta gabata ce Jam’iyyar PDP ta ba da sanarwar nada Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki a matsayin Daraktan Yakin Neman Zaben Shugabana Kasa na Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2019. Kakakin Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya fitar da sanarwar cewa Saraki ne Daraktan Kamfen neman zaben Atiku Abubakar. Saraki […]

An nada Saraki Daraktan yakin neman zaben Atiku

A ranar Talatar da ta gabata ce Jam’iyyar PDP ta ba da sanarwar nada Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki a matsayin Daraktan Yakin Neman Zaben Shugabana Kasa na Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2019.

Kakakin Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya fitar da sanarwar cewa Saraki ne Daraktan Kamfen neman zaben Atiku Abubakar.

Saraki yana daya daga cikin ’yan takara 12 da suka nemi PDP  ta tsayar da su takarar Shugaban Kasa tare da Atiku.

Shugaban Majalisar Dattawan, zai yi aiki da sauran daraktocin kamfen da za su kasance a karkashinsa da suka hada da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal na Arewa maso Yamma da Gwamnan Jihar Enugu, Dabid Umahi a Kudu masu Gabas da Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo a Arewa maso Gabas sai Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a Kudu maso Kudu da kuma Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom a Arewa ta Tsakiya, tare kuma da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da zai jagoranci kamfen a Kudu maso Yamma.

Kabiru Tanimu Turaki, wanda shi ma ya tsaya takarar ne zai zama mai ba da shawara kan harkokin shari’a ga kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel zai jagoranci kwamitin tara kudaden kamfe, sai kuma Femi Fani Kayode a matsayin Kakakin Kwamitin.