An nada Shugaban kasuwar kara ta Ilesha Barba a Kwara

Kasuwar  shanu ta Ilesha-Barba a Jihar Kwara ta samu sabon Shugaba, mai suna Alhaji Muhammadu Oro Kamba, da zai jagoranci al’amuran hada-hadar shanu a cikin wannan kasuwa, wacce tayi fice, musamman ga fatake daga jihohin makwabta, har da jumhuriyar Benin da suke rububin cin kasuwar a ranakun Litinin da Alhamis din kowane mako. daruruwan ‘yan kasuwar […]

An nada Shugaban kasuwar kara ta Ilesha Barba a Kwara
An nada Shugaban kasuwar kara ta Ilesha Barba a Kwara

Kasuwar  shanu ta Ilesha-Barba a Jihar Kwara ta samu sabon Shugaba, mai suna Alhaji Muhammadu Oro Kamba, da zai jagoranci al’amuran hada-hadar shanu a cikin wannan kasuwa, wacce tayi fice, musamman ga fatake daga jihohin makwabta, har da jumhuriyar Benin da suke rububin cin kasuwar a ranakun Litinin da Alhamis din kowane mako.
 daruruwan ‘yan kasuwar da suka hada da Hausawa da Bargawa da Fulani da Yarbawa da Bare-bari, har da mata a cikinsu ne suka amince da nadin Alhaji Muhammadu Oro Kamba, a matsayin sabon Shugaban Kasuwar ba tare da hamayya ba.
 Sarkin Hausawan Ilesha Barba, Alhaji Muhammad dan Ayashe, ya ce, “dukkan kabilun da suke gudanar da harkokin kasuwancin dabbobi a cikin wannan kasuwa sun amince da nadin sabon shugaban, saboda kyawawan halayensa da rikon amana, tare da hakuri da fafutukar ganin ya shawo kan matsalolin manoma da makiyaya, don zama lafiya a cikin wannan masarauta.”
Shi ma Sarkin Bargawa, Alhaji Usman, cewa yayi “irin kai-kawo da wannan mutumi Muhammadu Oro, ya rinka yi a shekarun baya wajen mika koke koken jama’arsa ga mahukumta, yana daga cikin cancantar da ta kai shi ga wannan mukami. Saboda haka muke yi masa addu’ar rokon Allah (SWT) yayi masa jagoranci. Su kuma ‘yan kasuwa, wajibi ne su zage damtse wajen bayar da hadin kai da goyon baya da salon jagorancin wannan mutumi.”
A jawabin sabon shugaban kasuwar shanu ta Ilesha, Barba Alhaji Muhammadu Oro Kamba, ya nuna matukar farin cikinsa ga jama’a da suka mara masa baya, tare da dora masa nauyi, wanda ya ce, zai yi duk abin da yake iyawa, domin ganin ci gaban kasuwar da samar da kudin shiga ga karamar hukuma da gwamnatin jihar domin bunkasa tattalin arziki.
Ya nemi jama’arsa su kasance masu bin doka da oda, domin samun zama lafiya.
“Duka wannan taron jama’a daga sassa daban daban na kasar nan da suka halarci wannan biki, sun samu damar zuwa ne saboda muna zaune lafiya,” inji shi.
Bikin ya samu halartar wakilan Gwamnatin Jihar Kwara da karamar Hukumar Baruten da wasu manyan ‘yan kasuwa daga jihohin Kebbi da Neja da Oyo da Ondo da Ogun da Edo.An gudanar da shagulgula, inda aka gayyaci mawakan kabilu daban-daban da suka shafe yinin wannan rana suna kade-kade da raye-rayen al’adun gargajiya.