An nada shugabannin riko na ‘yan kasuwar jihar Filato

A sakamakon cikar wa’adin shugabannin kungiyar  ’yan kasuwar Jihar Filato. An nada shugabannin riko mutum biyar da za su jagoranci kungiyar har ya zuwa lokacin da za a sake zaben sababbin shugabannin kungiyar. An dana shugabannin riko  ne a wajen wani taro da shugabannin kungiyar na kananan hukumar jihar 17, da aka  gudanar a ofishin […]

An nada shugabannin riko na ‘yan kasuwar jihar Filato

A sakamakon cikar wa’adin shugabannin kungiyar  ’yan kasuwar Jihar Filato. An nada shugabannin riko mutum biyar da za su jagoranci kungiyar har ya zuwa lokacin da za a sake zaben sababbin shugabannin kungiyar. An dana shugabannin riko  ne a wajen wani taro da shugabannin kungiyar na kananan hukumar jihar 17, da aka  gudanar a ofishin kungiyar da ke garin Jos.

Shugabannin rikon da aka nada sun hada da shugaban kungiyar na karamar Hukumar kuan, Pan Uthman Dafaan a matsayin shugaba, da shugaban kungiyar na karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji danAzumi Maigida Ibrahim a matsayin Sakatare, da shugaban kungiyar na karamar Hukumar Bokkos Mista Sunday Mabos a matsayin ma’ajiyi, da shugaban kungiyar na karamar Hukumar Shendam Mista Celement Kekur a matsayin sakataren kudi, da kuma shugaban kungiyar na karamar Hukumar Jos ta Kudu Muhammad Adamu a matsayin jami’in hulda da jama’a.

Da yake zantawa da jaridar Aminiya shugaban rikon Uthman Dafaan ya bayyana cewa, an nada su a matsayin shugabannin riko na kungiyar ne saboda  cikar wa’adin shugabannin kungiyar na jihar ta Filato, tun a watan 9 da ya gabata. Ya ce ayyukan da aka ba su su ne warware matsalolin kungiyar a wasu kananan hukumomin jihar,  tare  da shirya zaben sababbin shugabannin kungiyar. Ya yi kira ga ‘yan kasuwar jihar  su ba mu goyan baya da hadin kai, kuma su taya su da addu’a kan wannan aiki da aka ba su.

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50