An nada tsohon Kwamishinan Kudi Surajo Garba a matsayin Galadiman Karaye

Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar ll, ya nada tsohon Kwamishinan kudi na jihar Kano Alhaji Surajo Garba Karaye, a matsayin Galadiman Karaye kuma dan Majalisar Sarki a Masarautar Karaye da wasu ’yan majalisar masarautar. Yayin nadin, Sarkin na Karaye ya bukaci Sabon Galadiman na Karaye da sauran sabbin ’yan Majalisar Masarautar wadanda aka […]

An nada tsohon Kwamishinan Kudi Surajo Garba a matsayin Galadiman Karaye

Sabon Galadiman Karaye Alhaji Surajo Garba Karaye

Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar ll, ya nada tsohon Kwamishinan kudi na jihar Kano Alhaji Surajo Garba Karaye, a matsayin Galadiman Karaye kuma dan Majalisar Sarki a Masarautar Karaye da wasu ’yan majalisar masarautar.

Yayin nadin, Sarkin na Karaye ya bukaci Sabon Galadiman na Karaye da sauran sabbin ’yan Majalisar Masarautar wadanda aka nada wa rawani daban-daban, da su bayar da tasu gudunmawar wurin ciyar da masarautar gaba da tare da bayar da hadin kai wajen yi wa dokokin masarautar biyayya.

Sauran wadanda aka nada sun hada da tsohon Sanatan Kano ta Arewa, Sanata Bello Hayyatu Gwarzo a matsayin Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma daya daga cikin masu zabar Sarki a masarautar.

An kuma nada Alhaji Muhammad Mahraz a matsayin Wamban Karaye da Alhaji Shehu Kabiru Bayero a matsayin Barden Kerarriyar Karaye da Alhaji Balarabe Surajo a matsayin Chiroman Karaye sai kuma Alhaji lbrahim Ahmad Karaye a matsayin Iyan Karaye.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka nada, Galadiman Karaye Alhaji Surajo Garba Karaye, ya yi godiya ga al’ummar Masarautar Karaye bisa hadin kan da suke baiwa masarautar musamman a bangaren zaman lafiya.

Alhaji Surajo Garba ya kuma bukaci al’ummar masarautar da su baiwa jaririyar masarautar hadin kai da dukkan goyan bayan da ya dace ta yadda za ta bunkasa.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin nadin sun hada da Kwamishinan Shari’a na jihar Kano wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Matasa na jihar Kano, Alhaji Kabiru Ado Lakwaya da takwaransa na muhalli, Dokta Kabiru Ibrahim Getso.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos