An nada Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Magajiyar Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Hajiya Hadiza El-Rufa’i a matsayin Magajiyar Saminaka a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ta ziyarci karamar Hukumar Lere, don ganawa da matan karamar hukumar. Da yake jawabi a wajen, Mai martaba Sarkin Alhaji Musa Muhammad Sani ya ce […]

An nada Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Magajiyar Saminaka
An nada Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Magajiyar Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Hajiya Hadiza El-Rufa’i a matsayin Magajiyar Saminaka a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ta ziyarci karamar Hukumar Lere, don ganawa da matan karamar hukumar.

Da yake jawabi a wajen, Mai martaba Sarkin Alhaji Musa Muhammad Sani ya ce an nada Uwargidan Gwamnan, Magajiyar Saminaka ce, domin nuna godiya ga irin dimbin ayyukan raya kasa da Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya yi a yankin, da kuma kara dankon zumunci.

Ya yaba wa Uwargidan Gwamnan kan wannan ziyara da ta kawo yankin. Ya ba da tabbacin cewa al’ummar yankin za su ci gaba da bai wa gwamnatin Jihar Kaduna da Gwamnatin Tarayya goyon baya da hadin kai domin  cimma kudirorin bunkasa kasa da suka sanya a gaba.

A jawabin Uwargidan Gwamnan, ta bayyana cewa sun fara wannan ziyarce-ziyarce da karamar Hukumar Lere ne saboda muhimmancin da karamar hukumar take da shi.

Ta ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ayyuka da dama musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya a wannan karamar hukuma.

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta so ta yi ayyuka fiye da haka a wannan yanki, amma saboda yadda ’yan Majalisar Dattawa da suka fito daga Jihar Kaduna suka ki yarda a samo rance daga Bankin Duniya ya sanya ba a samu damar aiwatar da wannan kyakyawan kudiri ba,” inji ta.

Daga nan ta nuna matukar farin cikinta kan irin tarbar da aka yi mata. Ta ce a gaskiya ta yi matukar farin ciki ganin yadda dimbin matan wannan karamar hukuma suka fito suka tarbi ayarinta.

A jawabin Shugaban karamar Hukumar Lere, Alhaji Abubakar Buba ya bayyana cewa  babu shakka wannan ziyara da Uwargidan Gwamna ta kawo  wani babban karamci ne ga karamar hukumar.

Ya ba da tabbacin cewa al’ummar karamar hukumar za su bayar da kuri’a ga Shugaban kasa Muhammadu  Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i fiye da kowace karamar hukuma a yanki na1 na Jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

“karamar Hukumar Lere, karamar hukuma ce mai dimbin albarka musamman a aikin noma a Najeriya. Domin mu nuna miki cewa mu manoma ne, matan karamar hukumar nan sun baki kyautar buhun masara da buhun shinkafa  da buhun wake   da kuma rake.”