An neman mutum 11 ruwa a jallo kan hare-hare a Filato

Waɗanda ake nema ruwa a jallo na mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin da hukuma ke yi na tabbatar da zaman lafiya.

An neman mutum 11 ruwa a jallo kan hare-hare a Filato

Runduna ta musamman da ke wanzar da zaman lafiya ta Operation Safe Haven (OPSH) a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, ta ayyana neman wasu mutum 11 ruwa a jallo.

Ana neman su ne bisa zarginsu da hannu a hare-hare da kashe-kashe daban-daban, musamman a ƙananan hukumomin Barikin Ladi da Bassa da Bokkos da Riyom duk a jihar ta Filato.

Rundunar ta OPSH ta ce, ana neman mutanen ne domin su amsa tambayoyi dangane da zargin hannunsu a hare-haren da aka kai a wurare daban-daban a jihar.

Mataimakin Kwamandan Rundunar ‘Operation Safe Haven’, kuma mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, (DCP) Terzungwe Iyua, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar OPSH da ke Jos a ranar Juma’a, ya ce tukwici mai tsoka na jiran duk wanda ya taimaka wa hukuma wajen kama su.

Ya bayyana sunayen waɗanda ake neman da suka haɗa Muhammadu MP daga Bokkos da Muhammed da aka fi sani da MOPOL da Rabiu Ibrahim daga ƙauyukan Yelwa/Gashish/Nghar da Buba Sobe daga Tenti a Barikin Ladi da Senfos Inusa Gaine daga Zorgom da Nahaska Boderi shi ma daga Tenti, a Barikin Ladi.

Sauran sun haɗa da: Dudi Mohammadu daga unguwar Yamusa Bago ta ƙauyen Machambe, Habu Mohammadu daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe, Ja’afaru Matakala daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe; Hassan Waje daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe da Sanusi Dafor daga Ƙaramar hukumar Bokkos.

A cewar mataimakin kwamandan, duk da ƙoƙarin maido da zaman lafiya a yankin, waɗanda ake nema suna mayar da hannun agogo baya.

Ya kuma ƙara da cewa, a bisa ƙoƙarin rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’, jami’an rundunar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata munanan laifuka domin fuskantar shari’a ba.

“Mun ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri, wanda ya kai ga kashe wasu daga cikin masu laifin da suke da hannu a hare-haren.”