An nemi a gaggauta dawo da Kanu daga kasar Birtaniya
Wata kungiyar mai rajin kare ’yancin dan adam ta yi kiran da gaggauta dawo da shugaban kungiyar Biyafara ta IPOB, Mista Nnamdi Kanu zuwa gida Najeriya ko kuma ta shiga zanga-zanga. Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga Gwamnatin kasar Birtaniya da take boye Kanu bayan ya janyo mutuwar mutane da dama a Najeriya. Kungiyar […]

Wata kungiyar mai rajin kare ’yancin dan adam ta yi kiran da gaggauta dawo da shugaban kungiyar Biyafara ta IPOB, Mista Nnamdi Kanu zuwa gida Najeriya ko kuma ta shiga zanga-zanga.
Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga Gwamnatin kasar Birtaniya da take boye Kanu bayan ya janyo mutuwar mutane da dama a Najeriya.
Kungiyar tana mayar da martani ne kan bayanin da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya yi cewa Kanu ya gudu zuwa birnin Landan ta kasar Malesiya.
Tsohon Gwamnan jihar Abiyan ya ce “ba sojoji ba ne suka kama Kanu. Kanu ya sulale zuwa kasar Malesiya daga nan ya tafi kasar Birtaniya”.