An nemi a kawo karshen cin zarafin yara mata
Shugabar kungiyar kare hakkin mata ta Girls Green Effect da ke Enugu, Hadeezah Haruna-Ushie ta ce matukar ana son rage barazana da hadurran cin zarafin ’ya’ya mata da wasu mata musamman matasa ke fuskanta a kasar nan, sai an bullo da wata manhajar karantar da yara yadda za su rika kare kansu da kuma tsallake […]
Shugabar kungiyar kare hakkin mata ta Girls Green Effect da ke Enugu, Hadeezah Haruna-Ushie ta ce matukar ana son rage barazana da hadurran cin zarafin ’ya’ya mata da wasu mata musamman matasa ke fuskanta a kasar nan, sai an bullo da wata manhajar karantar da yara yadda za su rika kare kansu da kuma tsallake siradin cin zarafin.
Shugabar wadda ta ja hankalin cewa, a lura da yadda kodayaushe kotunan kasar nan ke cike da kararrakin cin zarafin yara kanana maza da mata, tab a da shawarar ce a Kalaba, yayin hira da Aminiya jim kadan da kammala gabatar da wata kasida a taron masu ruwa da tsaki da kungiyar kare mutuncin ’ya’ya mata wato GPI ta shirya ranar Litinin da ta gabata.
Ta ce kimanin yara sama da dubu 50 ne a sassan kasar nan da suke bukatar a koya masu yadda za su rika tunkarar iyayensu da wata matsala da ke damunsu ko kuma su iyayen su rika zama da yaran, su suna nuna masu yadda zamani ke tafiya domin su kare kansu daga duk wata barazana da ba ta zama alheri gare su ba. Ta ci gaba da cewa: “Ya kamata gwamnati ta bullo da wasu darussa da za a rika koya wa yara a makarantu, domin su san yadda za su rika kare kansu da kaucewa fadawa tarkon masu cin zarafin mata.”
Daga nan ta jaddada bukatar kowace jiha a kasar nan ta bullo da hanyar da ta ga za a iya karantar da yara darussan kare kansu. Ta bayyana cewa al’umma na da muhimmiyar gudunmawa da su ma za su iya bayarwa, musamman manya a unguwa, shugabannin matasa da kuma kungiyoyin sa kai, domin yakar masu bata tarbiyyar yara da ci masu zarafi; ba sai lallai an rika dora alhakin hakan kan iyaye kadai ba.
Daga karshe, shugabar ta nemi a kara tsaurara matakan tsaro a makarantu da kuma inda matasa ke zirga-zirga, domin kauce fadawa tarkon masu kama mutane suna garkuwa da su ko kuma kama ’yan mata suna cin zarafin su ko kuma fataucinsu.