An nemi al’umma su koma ga Allah

Sarkin Kano, Muhammdu Sanusi na II ya nemi al’ummar Musulmi a ciki da wajen Najeriya da su taimaka wajen gina kanana da manyan makarantun koyar da ilimin addinin Musulunci ga ’yan uwansu da ke zaune a masarautar Ondo.Sarkin ya nuna damuwa da ganin makarantar sakandare mallakar gwamnati guda daya kadai aka gina a cikin garin […]

An nemi al’umma su koma ga Allah
An nemi al’umma su koma ga Allah

Sarkin Kano, Muhammdu Sanusi na II ya nemi al’ummar Musulmi a ciki da wajen Najeriya da su taimaka wajen gina kanana da manyan makarantun koyar da ilimin addinin Musulunci ga ’yan uwansu da ke zaune a masarautar Ondo.
Sarkin ya nuna damuwa da ganin makarantar sakandare mallakar gwamnati guda daya kadai aka gina a cikin garin Ondo, ya ce, wajibi ne ga dukkan Musulmi ya bayar da gudunmawa mai tsoka domin a samu gina wa ’yan uwa wadatattun makarantu mallakar Musulmi zalla da samar da kayan aiki na zamani da kwararrun malamai a wannan masarauta da take matukar bukatar a kawo mata dauki, domin koyar da yara ilimin sanin addininsu.
Sarkin ya yi wannan kira ne a ranar Lahadin da ta gabata, a jawabinsa da Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar ya karanta a madadinsa, a wajen taron gamayyar kungiyoyin Musulmi da mabiyansu maza da mata da Gidauniyar At-Tanzil take shiryawa a garin Ondo a kowace shekara.
Shugaban taron, dan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Dokta Joseph Akinlaja, ya bayar da gudunmowar Naira dubu 200 ga gidauniyar tare da alkawarin ci gaba da bayar da tallafin kayan aiki domin ganin ta cin ma burinta.
Shugaban Gidauniyar At-Tanzil Islamic Foundation kuma limamin babban masallacin Allahu-Wahid a garin Ondo, Sheikh Abdul Rafi’u Ajiboye, ya nuna matukar farin cikinsa ga Sarkin Kano da dukkan Musulmi daga sassa daban-daban da suka amsa goron gayyata zuwa gamayyar taron na bana da gidauniyar ta shirya.
Sarkin Hausawan Ondo, Alhaji Abdulsalam Yusuf da sakatarensa Alhaji Musa Alhassan, su ne suka jagoranci daruruwan mutanensu da suka halarci wajen taron.