An nemi gwamnati ta sake gina kasuwar kayan gargajiya ta Abuja
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi gaggawar sake gina shagunan da suka kone a kasuwar sayar da kayan gargajiya ta Abuja sakamakon gobarar da ta auku a kasuwar a makon da ya gabata. Shugaban ’yan kasuwar, Kanayo Chukwumezie ne ya yi kiran a Larabar makon nan, yayin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya […]
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi gaggawar sake gina shagunan da suka kone a kasuwar sayar da kayan gargajiya ta Abuja sakamakon gobarar da ta auku a kasuwar a makon da ya gabata.
Shugaban ’yan kasuwar, Kanayo Chukwumezie ne ya yi kiran a Larabar makon nan, yayin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai musu ziyara don jajanta musu gobarar ta da auku a kasuwar a kwanannan.
Kanayo ya ce “mun tafka asara mai yawa, shaguna 36 ne suka kone sannan mun yi asarar kimanin Naira miliyan 400 zuwa 500. Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar sake gina kasuwar nan, tare da biyan diyya ga wadanda shagunansu suka kone don su ci gaba da gudanar da kasuwancinsu”. Inji shi.
Ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne dan siyasa na farko da ya je har kasuwar ya jajanta musu.
Saboda haka sai ya yi kira ga sauran jama’a da masu hannu da shuni da kuma gwamnati su taimaka musu don murmurewa daga bala’in da ya auka musu.
Shugaban, wanda ya yi zargin makarkashiya cikin tashin gobarar ya bayar da tabbacin cewa, ‘sun dauki matakan da suka kamata don kare sake aukuwar lamarin nan gaba.’
Da yake jawabi yayin da yakai ziyara kasuwar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin daukar matakan da suka kamata don ganin cewa gwamnati ta yi abin da ya kamata ga ’yan kasuwar.