An nemi gwamnatin tarayya ta gina xakunan karatu a karkara
An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gina xakunan karatun a yankunan karkara don bunkasa sha’awar karance-karance a tsakanin al’umma. Shugaban Xakin Karatu na garin Karshi wanda a Turance ake kira “Karshi Information Centre” Bawa Iliyasu Umar shi ne ya yi furucin yayin da Shugaban Hukumar da ke Lura da Xakunan Karatu na Qasa, Farfesa […]
An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gina xakunan karatun a yankunan karkara don bunkasa sha’awar karance-karance a tsakanin al’umma.
Shugaban Xakin Karatu na garin Karshi wanda a Turance ake kira “Karshi Information Centre” Bawa Iliyasu Umar shi ne ya yi furucin yayin da Shugaban Hukumar da ke Lura da Xakunan Karatu na Qasa, Farfesa Lenrie Aina ya ziyarta don ganewa idonsa ci gaban da xakin karatun ya samu.
Ya bayyana cewa kafa xakunan karatu zai taimaka qwarai da gaske wajen yaxa ilimi tare da bunqasa dabi’ar karatu a qasa baki xaya.
“Kamata ya yi gwamnati ta gina xakunan karatu kamar yadda ta tava gina cibiyoyin kallon talabijin a qasa baki xaya don yaxa ilimi da bunqasa karatu”. Inji shi.
Ya bayyana cewa xakunan karatun za su kasance cibiyoyin yaxa ilimi da wayar da kan jama’a tare da bayar da ilimi ga ’yan Najeriya.
Ya ce ’yan Najeriya musamman waxanda suke zaune a yankunan karkara za su fi samun bayanan gwamnati kuma hakan zai yi maganin jita-jita a tsakanin al’umma.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban Hukumar Da ke Kula da Xakunan Karatun Qasar nan, Farfesa Lenrie O. Aina ya bayyana jin daxinsa dangane da ci gaban da ya gani a xakin karatun na garin Karshi.
Ya bayyana cewa xakin karatu kamar na garin Karshi na daga cikin cibiyoyin da ke kore jahilci a tsakanin al’umma.
Ya bayyana cewa hukumarsa za ta tallafa wa xakin karatun da littatafai da bayar da horo ga ma’aikatansa da kuma haxa xakin karatun da sauran qungiyoyi masu zaman kansu.
Ya shawarci shugaban xakin karatun ya yi wa kantar littafan alama ta yadda duk wanda ya zo karatu zai sami saukin gane littafin da zai karanta.