An nemi iyaye su kula da tarbiyyar ’ya’yansu
Shugaban al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya bayyana takaici dangane da batun tabarbarewar tarbiyyar matasa ’yan asalin Arewa da ke Kudu, wanda ya ce sakacin iyaye ne tun da farko ya haifar da hakan kuma ya ce wasu iyayen ma akwai bukatar su gyara halayyarsu domin ’ya’yansu su yi koyi da su.Ya […]
Shugaban al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya bayyana takaici dangane da batun tabarbarewar tarbiyyar matasa ’yan asalin Arewa da ke Kudu, wanda ya ce sakacin iyaye ne tun da farko ya haifar da hakan kuma ya ce wasu iyayen ma akwai bukatar su gyara halayyarsu domin ’ya’yansu su yi koyi da su.
Ya ce: “A gaskiya tarbiyyar yaranmu da aka haifa a nan Kudu da wasu da ake zuwa da su daga Arewa tana kara gurbacewa, duk da cewa ba za mu iya mu ce dukkansu abin ya shafa ba, sai dai duk yadda ka ga halin da tarbiyyar yara take ciki to daga gidane amma kuma akwai wani abin da ke faruwa a sha’anin yara fandararru. Ya danganta ne da irin miyagun abokan da suke hulda da su a unguwa ko a makaranta, domin rashin sa musu ido. Saboda haka ya zama tilas ga iyayen su sa ido sosai ga shige da fice na ’ya’yansu a wannan karnin da muke ciki.”
Ya kawo misali da lokacin da gungun wasu matasa barayi dauke da makamai suka je masa gidansa a kwanakin baya har ya kai suka yi amfani da wannan damar suka farfasa masa gilasan motarsa. An yi zargin akwai hannun wani malamin addini dan Arewa, wanda yaronsa yana daya daga cikin wadannan barayi; a yayin da ’yan sanda suka samu labarin wannan dan malamin yana holewa a wani otel a cikin garin Benin. “Domin da labari ya zo mana a ranar Lahadi cewa daya daga cikin wadannan barayin an gan shi tare da abokansa suna sharholiya a wani otel sai na kai rahoto ga ’yan sanda, aka hada ni da ma’aikata muka je. Da ’yan kungiyarsu ta asiri suka gan ni da motata da ’yan sanda sai suka fada mu da jifa, suka farfasa mani gilasan mota.”
Shugaban ya ce amma wannan barazana ba ta sa ’yan sanda suka tsorata ba, sai da suka kama shi wannan barawon. Gaba dayansu ’yan Arewa ne sai dai yawancin su a nan Kudu aka haife su sun tashi da rashin tarbiyya. “Wannan dalilin ya sa nake kira tare da shawartar iyaye da shugabanni da mu tashi tsaye mu tabbatar da mun samar wa ’ya’yanmu nagartacciyar tarbiyya, ba wai mu zuba ido muna kallon komai yana ci gaba da tabarbarewa ba,” inji shi.