An nemi jami’an alhazai su ji tsoron Allah

Sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna Alhaji Sani Dalhatu Musa ya nemi ma’aikatan hukumar su kara kaimi a kan aikinsu tare da jin tsoron Allah. Ya ce ma’aikatan dole su fahimci cewa akwai bukatar a rika kulawa ta musamman ga maniyyata da ke nemo kudinsu da kyar domin biyan kujerar Hajji. Shugaban […]

An nemi jami’an alhazai su ji tsoron Allah
An nemi jami’an alhazai su ji tsoron Allah

Sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna Alhaji Sani Dalhatu Musa ya nemi ma’aikatan hukumar su kara kaimi a kan aikinsu tare da jin tsoron Allah.

Ya ce ma’aikatan dole su fahimci cewa akwai bukatar a rika kulawa ta musamman ga maniyyata da ke nemo kudinsu da kyar domin biyan kujerar Hajji.

Shugaban ya yi kiran ne lokacin da yake amsar ragamar mulkin hukumar a ranar Talatar da ta gabata.

Ya bayyana cewa kowa ya sani cewa duk abin da ya aikata zai yi bayani a gaban Allah a ranar gobe Kiyama, wanda hakan ya sa tilas a rika saka tsoron Allah cikin aikin domin a samu tsira.

“Ina mika godiyata ga Allah ga dukkan ni’imomi da Ya yi min kuma wannan aiki da aka ba ni nauyi ne babba amma na yi imani Allah zai taimake mu. Haka kuma da goyon bayanku za mu samu ci gaba in Allah Ya yarda.

“Domin a yanzu an samu canje-canje da dama a aikin Hajji don haka mu ma za mu yi kokari matuka wajen ciyar da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar nan gaba domin babu wanda zai ce ya san komai a aikin Hajji amma da taimakonku, ma’aikata Allah zai taimake mu,” inji shi.

Alhaji Sani Dalhatu ya bayyana cewa kofarsa a bude take wajen daukar shawarwari domin ciyar da hukumarsa gaba.

A jawabin tsohon Shugaban Hukumar da ya bar gado, Imam Hussaini Suleiman Tsoho Ikara ya bayyana aniyarsa ta taimaka wa sabon shugaban da shawarwarin da za su taimake shi.

Ya kuma nemi ma’aikatan hukumar su guji kwadayi domin a cewarsa kwadayi ke janyo wulakanci da zubar da mutunci. Sannan ya yaba wa ma’aikatan hukumar a bisa goyon baya da suka ba shi lokacin mulkinsa.