An nemi magidantan Saudiyya su fara shirin shiga dakin girki a watan azumi

Wata marubuciyar makala a jaridar Al-watan ta kasar Saudiyya, ta yi kira ga magidanta kan lalle su yi shirin shiga dakin girki don taimaka wa matansu, musamman a cikin watan azumin Ramadan.A cikin makalar da ta rubuta, ta bayyana cewa maza da mata masu koshin lafiya suna azumtar watan Ramadana, ta hanyar kaurace wa abinci […]

An nemi magidantan Saudiyya su fara shirin shiga dakin girki a watan azumi
An nemi magidantan Saudiyya su fara shirin shiga dakin girki a watan azumi

Wata marubuciyar makala a jaridar Al-watan ta kasar Saudiyya, ta yi kira ga magidanta kan lalle su yi shirin shiga dakin girki don taimaka wa matansu, musamman a cikin watan azumin Ramadan.
A cikin makalar da ta rubuta, ta bayyana cewa maza da mata masu koshin lafiya suna azumtar watan Ramadana, ta hanyar kaurace wa abinci da abin sha, tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana. Kuma iyalai kan shirya abinci na alfarma a yammacin ranakun; irin wannan abinci ana shafe sa’o’i ana shirya shi. “Yanzu tunda Ramadan ya karato, dakin girki zai zamo wani muhimmin wuri a cikin gida,” kamar yadda Taghreed Al Tamimi ta rubuta a cikin jaridar kullum ta al-Watan da ake bugawa a kasar Saudiyya. “dimbin aiki na karuwa, ta yadda maigida bai san abin da aka yi ba. Don haka, lokaci ya yi da magidanta a kasar Saudiyya za su yakice al’ada, su fara shiga dakin girki, don taimaka wa uwargida,” kamar yadda yake kunshe a makalar da rubuta, mai taken “Magidancin Saudiyya mai adawa ne da dakin girki.”
Taimakon da maigida zai yi wa matarsa ba wani mai yawa ba ne, sai dai ta haka ne zai fahimci dimbin aikin da uwargida ke yi, kafin a acika masa faranti da kayan makwalashe da tande-tande da lashe-lashe, kamar yadda ta bayyana.
“Abin takaici ne, ganin cewa a wasu al’ummomin, maza ba sa yin adawa da dakin girki, yayin da wasu magidantan ko dafa kwai bas u iya ba, ballanta hada kofin shayi,” injita.
Taghreed ta ce tunda ana sa ran azumin Ramadan zai kama a ranar tara ga watan Yulin bana, wata dama ce ta samu ga maza su kyautata dangantakarsu da dakin girki.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda