An nemi mawakan siyasa su rike akida a sana’arsu

Wani fitaccen mawakin siyasa da ke Jihar Kano, Alhaji Musa Saye ya ce rashin cikakkiyar akida ya sa ake samun koma baya a fannin wakar siyasa, musamman a bangaren mawakan jam’iyya da kuma iyayen gidajensu.Ya yi wannan tsokaci ne cikin zantawarsu da wakilinmu, inda ya ce idan dukkanin mawakan siyasa za su rike akidar jam’iyyar […]

An nemi mawakan siyasa su rike akida a sana’arsu
An nemi mawakan siyasa su rike akida a sana’arsu

Wani fitaccen mawakin siyasa da ke Jihar Kano, Alhaji Musa Saye ya ce rashin cikakkiyar akida ya sa ake samun koma baya a fannin wakar siyasa, musamman a bangaren mawakan jam’iyya da kuma iyayen gidajensu.
Ya yi wannan tsokaci ne cikin zantawarsu da wakilinmu, inda ya ce idan dukkanin mawakan siyasa za su rike akidar jam’iyyar da suke bi, ko shakka babu za su kasance a sahun gaba wajen gyaran siyasa a tsarin dimokuradiyyar kowane zamani.
Sannan ya nuna cewa mafiya yawan mawakan siyasa yanzu sun kasance marasa akida kuma ba su da iyayen gida na dindindin saboda gudun rasa abin duniya daga hannun ’yan siyasa, wanda hakan ya canza fasalin tsarin wallafar siyasa zuwa neman abin duniya ko kuma gindin zama a sha’anin wallafa.
Don haka ne ma a cewarsa, a yau ake kallon mawakan jam’iyya tamkar wasu marasa ’yanci ko kuma wani dandali na bunkasa dimokuradiyya saboda rashin akida da daukar wallafa a matsayin bada gudunmawa ga ci gaban mulkin dimokuradiyya.
Mawakin ya jaddada cewa idan mawakan siyasa suka rungumi akida ko shakka babu za su zamo abin alfahari, sannan za su ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai ban sha’awa saboda wannan akida da suka rike a sana’arsu ta wallafar wakokin jam’iyya.
Haka kuma ya ba da misali da cewa masu wakokin siyasa suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tsarin dimokuradiyya a duniya, don haka yana da muhimmanci su kasance masu akida da manufofi na wayar da kai da fadakar da al’umma irin yadda manufofin jam’iyyunsu  suke tun kafa jam’iyyun zuwa yakin neman zabe da kuma bayan kafa gwamnati.
Bisa haka ne shahararren mawakin ya bukaci daukacin mawallafa na siyasa da su kasance masu akida kan jam’iyyunsu, duk da cewa al’amuran wakar siyasa sun canza saboda yadda su kansu ’yan siyasar ke canza wa mawallafan akida cikin hikima da kasuwar bukata, wanda sai an yi da gaske kafin a kawar da wannan halayya.
Dangane da mutanen da yake tare da su a siyasance kuwa, Musa ya sanar da cewa tun da ya fara siyasa a shekara ta 1992, har yau bai canza akidarsa ba, sai dai a same shi a inda yake tun da fari, inda ya bayyana cewa ya fara siyasa ne da rusashshiyar jam’iyyar NRC kuma tun daga mazabar Saye cikin yankin karamar Hukumar Bichi, Jihar Kano a matsayin shugaban jam’iyya na wannan mazaba kafin daga bisani ya ci gaba da wakar siyasa har zuwa yanzu.
Daga karshe, mawallafin ya yi fatan alheri ga ’yan uwansa mawallafa wakokin siyasa da ke fadin kasar nan, tare da yin godiya ta musamman ga iyayen gidansa, wadanda suke siyasa tare bisa akida iri daya da kuma manufofi daya na bunkasa dimokuradiyya a dandamalin akidar ci gaban wannan kasa.