An nemi mutane su koma ga Allah

An bayyana abubuwa uku da cewa su suka fi zama babban kalubalen da ya fi addabar Musulunci da Musulmi kuma mafi girma, wadanda suka hada da jahiltar addini, son zuciya da kuma rashin tsayuwa wajen bauta wa Allah shi kadai. Assheik Muhammad Bashir Adam, malamin addinin Musulunci na kungiyar Izala mai hedkwata Jos ne ya […]

An nemi mutane su koma ga Allah

An bayyana abubuwa uku da cewa su suka fi zama babban kalubalen da ya fi addabar Musulunci da Musulmi kuma mafi girma, wadanda suka hada da jahiltar addini, son zuciya da kuma rashin tsayuwa wajen bauta wa Allah shi kadai.

Assheik Muhammad Bashir Adam, malamin addinin Musulunci na kungiyar Izala mai hedkwata Jos ne ya furta haka a Kalaba, yayin zantawarsa da Aminiya lokacin da ya kai ziyara ta karfafa dankon zumunci cikin wannan mako.

“Abin da ma yake kawo irin wannan kalubale shi ne, na farko rashin sanin addini, sannan na biyu kuma shi ne son zuciya na uku kuma shi ne rashin tsayuwa a gabatar da bauta tsakani ga Allah.”

“Ga kuma gurbacewar mu’amala tsakaninmu. Za ka ga wani lokaci ma tsakanin miji da mata a yi ta samun matsala ko kuma tsakanin makwabci da makwabci ko tsakanin abokin harka ta kasuwanci da dai sauransu. Wani lokaci ma tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba, a takaice su ne kadan daga cikin abubuwan da suke haddasa matsaloli, ” inji shi.

Da aka tambaye shi hanyoyin magance wadannan kalubale, sai ya ce: “Hanyoyin magance su, lallai dai a koma ga Allah, a dukufa a yi karatu tsakani da Allah sannan kuma iyaye su tsaya tsakani da Allah su lura da tarbiyyar ’ya’yansu, sannan kuma shugabanni su yi adalci tsakaninsu da talakawansu kuma su talakawa su yi biyayya ga shugabanninsu; kowa ya zauna lafiya da dan uwansa, tun da Allah Ya hada su mu’amala tare. Kada Musulmi ya zalunci Musulmi, shi ma kuma kada ya zalunci wanda ba Musulmi ba. Kowa a yi masa adalci, su ma wadanda ba Musulmi ba a yi musu adalci, domin su fahimci cewa Musulunci addini ne na adalci.”

Daga karshe, malamin ya yi kira ga alummar Musulmi da cewa duk abin da za su yi, su yi don Allah, sannan kuma akwai bukatar Musulmi su ci gaba da addu’ar zaman lafiya a duk inda suka kasance, har tsakaninsu da ma wadanda ba Musulmin ba.