An nemi wadanda matar Shugaban kasa ta bai wa amana su ji tsoron Allah
Shugabar kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awa ta Najeriya, reshen Jihar Neja Malama Rabi danladi Makun ta yi kira ga wadanda matar Shugaban kasa Hajiya A’isha Muhammadu Buhari ta bai wa amanar rarraba kayan masarufi su sanya tsoron Allah wajen isar da sakonta ga mabukata.Malama Rabi danladi Makun ta yi wannan kira ne yayin da take […]
Shugabar kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awa ta Najeriya, reshen Jihar Neja Malama Rabi danladi Makun ta yi kira ga wadanda matar Shugaban kasa Hajiya A’isha Muhammadu Buhari ta bai wa amanar rarraba kayan masarufi su sanya tsoron Allah wajen isar da sakonta ga mabukata.
Malama Rabi danladi Makun ta yi wannan kira ne yayin da take tattaunawa da wakilinmu a Minna a karshen makon jiya, inda ta bayyana takaicinta kan yadda mabukata suke ta korafin cewa kayan masarufin ba su kaiwa gare su.
“Babban abin takaici wasu bayanan da muke samu ta kafofin watsa labarai babu dadin ji, domin kuwa da dama daga cikin wadanda aka yi wa tanadin kayan masarufin ba su gani a kasa da zarar an bar wurin taron,” inji ta
Shugabar ta ci gaba da cewa, “Gaskiya ban san abin da wadansu daga cikin irin wadannan mutane za su fada wa Allah ba a gobe kiyama. Baiwar Allah nan ta hana idonta barci ta kukkutsa wurare daban-daban ta samo gudunmawa daga wurin mutanen da take ganin za su iya taimakawa, ta kawo ta mika amana, amma maimakon mutum ya san ba zai iya ba, ya ce mata ba zan iya ba, sai ya amsa ya bi son ransa, ko kuma ya ki rabawa baki daya.”
Ta ce tura tallafin da matar Shugaban kasar ta yi wurare daban-daban ya nuna cewa wannan kasa ta samu uwa tagari wadda ta damu da ciwon da ke damun ’ya’yanta musamman wadanda aka tarwatsa a shiyyar Arewa maso Gabas sanadin barnar da ’yan kungiyar Boko Haram suka haddasa.
Ta ce Hajiya A’isha Buhari ta yi rawar gani da ta tuna da Jihar Neja har ta turo tallafin kayan abinci ta hannun matar Gwamnan Jihar, Dokta Amina Abubakar Bello wadda ta tabbatar mutanen da suka dace sun ci moriyar tallafin. Sai ta bukaci ’yan Najeriya su kasance masu tausayin juna. “Kamata ya yi masu hannu da shuni su ci gaba da taimaka wa wadanda suke cikin kuncin rayuwa musamman a wannan lokaci na rashin tabbas da kuma tsadar kayan masarufi a kasar nan,” inji ta.