An nuna wa kurciya baka
Duk da cewa duniya ta yaba wa tsohon Shugaban kasa, Dokta Goodluck Ebele Jonathan saboda da abin da ake ganin tankar kyaun kai ne bisa ga amincewarsa da sakamakon zaben watan Maris, inda ya sha kasa, amma jam’iyyarsa ta PDP ba ta hakura ba, balle ta san annabi ya faku, za a yi tashin duniya, […]
Duk da cewa duniya ta yaba wa tsohon Shugaban kasa, Dokta Goodluck Ebele Jonathan saboda da abin da ake ganin tankar kyaun kai ne bisa ga amincewarsa da sakamakon zaben watan Maris, inda ya sha kasa, amma jam’iyyarsa ta PDP ba ta hakura ba, balle ta san annabi ya faku, za a yi tashin duniya, sai ta ci gaba da daukan matakan bata abokin adawar Jonathan, tana shafa masa kashin kaji da kuma kokarin watsa kasa a garinsa. Wannan abin da jam’iyyar ke yi a halin yanzu na nuna adawa mara ma’ana, cike da hassada da kuma nuna bakar kiyayya ya tabbatar da cewa dole ba yarda ne ba, idan sakamakon zabe ya tilasta shugabanninsu amincewa, to ai ba dole ne su yarda ba.
Batutuwa guda uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa idan ya kai ga nasarar lashe zabe, su ne suka zame abubuwa guda ukun da a halin yanzu ke sanya jam’iyyar PDP da jiga-jigan ’ya’yanta karkarwa da makyarkyatar tsoron fuskantar sakamakon ayyukansu. Dangane da haka ne suka tsara hanyoyin yin fito-na-fito da shi da niyyar taka masa burki da kuma bakanta shi a idanun jama’a da rage masa kima a idanun sauran kasashen duniya wadanda suka tabbatar da cewa a shirye yake ya komo wa Najeriya da martabarta.
Shugaba Muhammadu Buhari ya dukufa ka’in da na’in, jim kadan bayan rantsar da shi, don daukan matakan da suka dace na kawar da ta’addaci da yin maganin ‘yan ta’adda, ya kuma fara aiwatar da kyawawan manufofinsa na yaki da zalunci da ha’inci da kuma cin hanci, sa’annan ya yunkura don aiwatar da tsare-tsarensa na farfado da tattalin arzikin kasar ta yadda hakan zai fitar da dimbin jama’a daga kangin talauci da kuma rashin aikin yi.
A tashin farko na hankoron kawo masa cikas, wasu tsirarun ‘yan jam’iyyar Shugaba Buhari sun hada kai da baki don yi wa jam’iyyar APC da ke da rinjaye shiga hanci da dukunkune, yayin da suka yi zamba cikin tsarin zaben sabbin shugabanni, aka zabi wadanda jam’iyyar adawa ta tabbatar za su dinga ba ta cikakken goyon baya don dakile dukkan wasu manufofi da shawarwarin da za a kawo gaban majalisun don yaki da ha’inci da cin hanci. Dangane da haka ne ma aka yi gamin gambiza a shugabancin Majalisar Dattijai, tsakanin jam’iyya mai rinjaye, wacce ita ce ya kamata ta fitar da shugaba da mataimakinsa, da kuma jam’iyyar PDP wacce ta taimaka aka tafka magudin da yanzu haka ya zame wa jam’iyyar babbar matsala. An ce jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne, wadanda ke da hannu dumu-dumu cikin badakalar tallafin man fetur da kuma wadanda suka dulmuya hannayensu har iyaka hammata cikin kwatanniyar dukiyar talakawa, suka yi ta dumbuzowa, suka taimaka aka aikata waccan ta’asar ta zaben shugabannin majalisun biyu.
To, ana wata, sai ga wata! Jam’iyyar PDP na neman warware waccan wala-walar da aka kada mata a majalisa, ta kuma dauki mara cin, sai kuma ga wata sabuwar fitina can, sabuwa fil, ta kunno kai don a shafawa Shugaba Buhari kashin kaji, a kuma nuna cewa ai gara jiya da yau dangane da matsalar tsaron da ya kasance tamkar mari mai tayar da na zaune tsaye. A yanzu haka hankulan ‘yan Arewacin kasar nan idan sun kai dubu duka a bace suke ganin yadda babu kwanciyar hankali da lumana, ko kuma tabbas dangane da tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu. A ‘yan kwanakin da suka gabata, cikin wata mai tsarki na azumi, kuma mai alfarama, an tayar da fitintinun da suka tabbatar da cewa an fake ne da guzuma, ana ta harbin karsana, an rufe kiyayyar siyasa ce da taguwar ta’addanci domin a samu sukunin hargitsa lissafi da wargaza manufofin gwamnatin Muhammadu Buhari, da kuma karya masa irli.
Matakan da ya dauka jim-kadan bayan hawansa mulki sun yi nuni da cewa a shirye yake don kawo karshen masifar Boko Haram don kowa da kowa ya huta da matsalolin da hakan ya haifar. To, amma dalilai guda biyu na kawo masa cikas dangane da haka. Da farko dai ana so a ci gaba da tayar da fitintinun don a nuna gazawarsa wajen murkushe ‘yan ta’addan, a kuma nuna cewa shi ma lusari ne kaman tsohon Shugaban kasa, ba zai iya tabuka komai ba. Na biyu kuma shi ne kwamandojin askarawan Najeriya ba za su so a ce an kammala waccan dambarwar ba da ‘yan Boko Haram, domin ta nan ne suke samun daman yin cuwa-cuwa da mundahana wajen sayen makaman yaki da kuma kudaden tufatarwa da ciyar da sojoji, musaman ma wadanda suke shingayen tsaro da ke bisa manya da kananan hanyoyin mota a fadin tarayyar kasar, wadanda a yanzu aka kawar da su. Ana zargin cewa akwai hannayen wadancan jami’an cikin tashin bama-bamai, kuma muddin ba korarsu aka yi ba to da wuya a ga bayan rikita-rikitar da ake zargin suna haddasawa a halin yanzu.
Har yanzu an kasa shawo kan matsalolin man fetur da wutar lantarki, domin kuwa wadanda ke da alhaki wajen samuwar mai faca-faca ne suka haddasa matsalolin da ke janyo karancinsa a halin yanzu, kuma su ne wadanda idan binciken hukumar man fetur ya yi tsanani za a fahimcin irin badakalar da suka haddasa. Saboda haka nan suna nan suna ci gaba da daukan matakan karasa gurgu da tadiye, ta hanyar taimakawa wadancan shugabannin majalisar da kada su amince da dukkan yunkurin da za a yi don yin gyare-gyaren da ba za su dadada masu ba a dokar Sarrafa Maikatar Manfetur, wacce ake kira Petroleum Industry Bill, PIB don a tsame hannayensu daga irin cuwa-cuwar da suke cabawa.
To, koma dai menene makiya zaman lafiya da karuwar arzikin talakawa za su yi don durkusar da gwamnatin Buhari da kuma kai shi kasa, shi kansa, talakawan da suka zabe shi sun rigaya sun fahimci haka, kuma ba za su ba su dama ba, domin kuwa an rigaya an nuna wa kurciya baka.