An raba gidajen sauro dubu 224 a karamar Hukumar Lere
Shugaban sashin kiwon lafiya na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Muhammed Sa’adu Kagarko ya ce sun raba gidajen sauro dubu 224 da 779 a cikin kwana biyar da suka yi suna aikin raba gidajen sauro a karamar hukumar. Alhaji Sa’adu Kagarko ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a […]
Shugaban sashin kiwon lafiya na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Muhammed Sa’adu Kagarko ya ce sun raba gidajen sauro dubu 224 da 779 a cikin kwana biyar da suka yi suna aikin raba gidajen sauro a karamar hukumar.
Alhaji Sa’adu Kagarko ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Saminka, inda ya ce sun samu gidajen sauro ne daga hukumar yaki da zazzabin cizon sauro ta kasa.
Ya ce an kirkiro shirin raba gidajen sauro a shekarar 2009 a Najeriya, don a yaki zazzabin maleriya da ke illa ga kananan yara da mata masu juna biyu.
Ya yaba wa al’ummar karamar hukumar kan yadda suka rungumi shirin hannu bibbiyu, inda ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar su yi amfani da gidajen sauro, kuma su guji sayar da su. Ya ce su rika shanya gidajen sauron a inuwa su yi awa 24, kafin su yi amfani da su.