An raba wa iyalan ’yan sandan da suka rasu sama da N2bn
Olukoyode ya hori iyalan da suyi amfani da kudin yadda ya kamata.
Babban Sufeton ’yan sanda na kasa, Olukayode Egberokun, a jiya Alhamis ya mika cakin kudi ga iyalan jami’an rundunar da suka riga mu gidan gaskiya.
An yi bikin raba wa iyalai 613 cakin kudin na fiye da naira biliyan biyu a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.
- Ba za mu karɓo bashin ketare don cike gibin Kasafin Kudin 2024 ba — Ministan Kudi
- Ganduje da Abdullahi Abbas sun shirya tayar da tarzoma a Kano — NNPP
An samar da kudin ne ta hanyar shirin inshoran rai na jami’an rundunar ’yan sanda da Gwamnatin Tarayya ke ware wa kudi, da kuma shirin kula da iyalan jami’an rundunar, wanda rundunar ’yan sanda da kanta take warewa kudi.
Olukoyode ya hori iyalan da su yi amfani da kudin yadda ya kamata, inda ya kara da cewa “ana ba da kudin ne domin tausaya wa iyalan jami’anmu da muka rasa, da kuma ba su abin da za su tafiyar da rayuwar yau da kullum.”