An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe

An buƙaci tabbatar da cewa manoma a kowane lungu da saƙo na jihar suna noman amfanin gona da iri masu inganci.

An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe

Gwamnatin Yobe ta raba wa ma’aikatan gona babura guda 200 domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar.

Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa, Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa baburan ga waɗanda suka rabauta.

Ya ce an yi rabon baburan ne domin tallafa wa ayyukan ma’aikatan da kuma bunƙasa noman zamani a jihar ta hanyar sabbin dabaru da kayan aiki.

Goniri ya ce ma’aikatar gona za ta sa ido kan yadda ma’aikatan da ke aikin faɗaɗa ayyukan noma ke yi domin tabbatar da cewa manoma a kowane lungu da saƙo na jihar suna noman amfanin gona da iri masu inganci.

A cewarsa, an horas da ma’aikatan da za su yi aiki domin kyautata alaƙa tsakanin masu bincike da manoma, don haɓaka samar da kayayyaki, tabbatar da samar da abinci, da kuma inganta rayuwar manoma.

A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Inuwa Gulani, ya ce jami’an ma’aikatar aikin gona za su taimaka wa manoma wajen yanke shawara kan kirkire-kirkire da fasaha kan harkokin noma na zamani.

Ya ce ma’aikatan za su kuma taimaka wa manoma wajen samun sabbin bayanai da fasahohin zamani, inda ya ce shirin zai taimaka wa manoman wajen inganta sana’o’insu, da inganta rayuwar su, da tabbatar da samar da abinci ga al’umma.