An rada Tinubu don sasanta ‘yan APC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada tsohon gwamnan Jihar Legas, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam’iyyar APC mai mulki. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Bola Tinubu zai shugabanci kokarin […]

An rada Tinubu don sasanta ‘yan APC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada tsohon gwamnan Jihar Legas, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam’iyyar APC mai mulki.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Bola Tinubu zai shugabanci kokarin ganawa da sasanta wa da kuma inganta zaman da ake yi a APC. A cewar sanarwar, wasu daga cikin abubuwan da ake sa ran jigon jam’iyyar ta APC zai aiwatar, sun hada da dinke barakar da ke tsakanin mambobi da shugabanni da masu rike da mukaman jam’iyyar a jihohi da kuma kasa baki daya.

Wadanda suka fi fitowa fili su ne rigimar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsakanin gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da bangaren Sanata Shehu Sani. Haka kuma ana sa ran kwamitin na Bola Tinubu zai yi sulhu a rikicin APC da ke faruwa a Zamfara da Oyo da Kogi da dai sauransu.