An rage farashin man fetur a Nijar

Nijar ta ce matakin zai soma aiki ne daga ranar 23 ga watan Yuli.

An rage farashin man fetur a Nijar

An ƙara farashin man fetur a Najeriya

Gwamnatin soji da ke mulki a Jamhuriyyar Nijar ta sanar da rage farashin man fetur a fadin ƙasar.

Gwamnatin ta rage farashin fetur ne ƙasa daga CFA 540 zuwa CFA 499, haka ma an rage farashin dan dizel zuwa CFA 618 daga CFA 668.

BBC ya ruwaito cewa Gwamnatin ta Nijar ta ce matakin zai soma aiki ne daga ranar 23 ga watan Yuli.

Gwamnatin sojin Nijar ta ce manufar rage farashin shi ne rage wa ’yan ƙasa raɗaɗi musamman samun sauki kan farashin sufuri da na kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Sai dai masu nazari kan al’amuran yau da kullum na ganin ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki na tabbatar da ganin ’yan kasuwa a kasar sun sauko da farashin kayayyaki.

A jiya Laraba ce Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sanar cewa zai saki dala miliyan 71 ga kasar Nijar.