An rage kuɗin wutar lantarki a Ghana

Ragin kuɗin wutar na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi karin kuɗin ruwa a Ghana.

An rage kuɗin wutar lantarki a Ghana

Hukumar da ke sa ido kan biyan biyan kudaden wuta da ruwa da sauran kayan amfani a kasar Ghana (PURC), ta rage kudin wutar da za a biya a kasar da kashi 1.52 cikin 100.

Sai dai ragin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta PURC ta yi karin kudin da za a rinka biya na ruwa a kasar da kashi 0.34 a cikin 100 a rubu’i na karshe na shekarar 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ghana ya ruwaito cewa wannan sabon gyaran da aka yi a farashin wuta da ruwa zai soma aiki ne daga 1 ga watan Disambar 2023 zuwa 29 ga watan Fabrairun 2024.

Sakamakon wannan ragin da aka yi, masu zama a unguwannin marasa galihu za su soma biyan Cedi 0.6348 a duk kWh idan aka kwatanta da 0.6446 da suke biya a halin yanzu.

Sai kuma sauran jama’a za su rinka biyan Cedi 1.40 a duk kWh daga Cedi 1.42 da suke biya a baya.

Ga kuma masu amfani da ruwa a cikin gidaje, za su soma biyan Cedi 4.7401 a duk m3 daga 1 ga watan Disamba a maimakon 4.7239 da suke biya a halin yanzu.

Sai kuma wuraren da ba gidaje ba za su rinka biyan Cedi 14.19 a duk m3 a maimakon 14.1394 da uske biya, sai kuma wuraren kasuwanci za su rinka biyan Cedi 25.38 daga 25.2962 da suke biya.

Harin Borno: Mun kashe ’yan ta’adda 34, mun rasa dakaru 6 – Sojoji

Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

G-Fresh da Babiana sun nemi a saki Baɗejo

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa