An rantsar da Fayemi Gwamnan Ekiti karo na biyu

A ranar Talatar da ta gabata ce aka rantsar da sabon Gwamnan Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi karo na biyu. Dokta Fayemi, wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka yi a Jihar Ekiti a watan jiya a karkashin Jam’iyyar APC, inda ya kayar da Mataimakin Gwamnan Jihar kuma dan takarar  PDP, Farfesa Kolapo Olusola da […]

An rantsar da Fayemi Gwamnan Ekiti karo na biyu

A ranar Talatar da ta gabata ce aka rantsar da sabon Gwamnan Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi karo na biyu. Dokta Fayemi, wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka yi a Jihar Ekiti a watan jiya a karkashin Jam’iyyar APC, inda ya kayar da Mataimakin Gwamnan Jihar kuma dan takarar  PDP, Farfesa Kolapo Olusola da sauran ’yan takara daga wasu jam’iyyu.

Gwamnan mai shekara 53 ya karbi rantsuwar kama aiki ne daga Babban Jojin Jihar, Mai shari’a Ayodeji Daramola a Ado-Ekiti babban birnin jihar. Sabon Gwamnan zai yi mulki na wa’adi daya ne don kammala shekara takwas da tsarin mulki ya gindaya, kasancewar ya taba zama Gwamna daga 2010 zuwa 2014.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci Shugaban Kasa Muhamadu Buhari a wajen bikin. Kuma taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Kaduna, Nasir El-Rufa’i da na Oyo, Abiola Ajumobi da na Kebbi, Atiku Bagudu da kuma na Legas, Akinwunmi Ambode da na Bauchi, Mohammed Abubakar.

Rantsuwar ta zo ne a daidai lokacin da tsohon Gwamnan Jihar, Ayo Fayose ya kai kansa ga Hukumar EFCC kamar yadda ya yi alkawari zai yi idan ya sauka daga mulki. Sai dai kuma Fayose ya kwashi ’yan kallo yayin da ya isa ofishin EFCC a ranar Talatar tare da dandazon jama’a ciki har da wadansu kusoshin Jam’iyyar PDP, da suka hada da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode.

Fayose ya shiga ofishin EFCC sanye da riga mai dauke da kalmomin da ke cewa: “EFCC, ga ni na zo,” cikin Ingilshi, kuma dauke da jakunkuna biyu da suke dauke da kayan da zai bukata a yayin zaman da zai yi a ofishin EFCC da suka hada da tabarmar kwanciyar da filo.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa