An rantsar da sababbin kwamishinonin Jihar Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya hori sababbin kwamishinonin jihar takwas da ya rantsar su kawo kyakkyawan canji da zai inganta rayuwar al’ummar jihar.Gwamna Abubakar Bagudu ya yi wannan kira ne a wajen bikin rantsar da sababbin kwamishinonin jihar, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.Gwamna Bagudu ya yi gargadin cewa lokacin da […]
Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya hori sababbin kwamishinonin jihar takwas da ya rantsar su kawo kyakkyawan canji da zai inganta rayuwar al’ummar jihar.
Gwamna Abubakar Bagudu ya yi wannan kira ne a wajen bikin rantsar da sababbin kwamishinonin jihar, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
Gwamna Bagudu ya yi gargadin cewa lokacin da shugabanni za su shiga ofis da burin azurta kawunansu ya wuce, ya yi kiran su zamo masu qwazo da tsaida gaskiya wajen sauke nauyin da al’umma suka dora musu, ta wajen yin adalci tare da fuskantar dimbin matsalolin da suke damun jama’a, musamman ganin sababbin kwamishinonin ba sababbin kamu ba ne a aikin gwamnati yawancinsu sun dade cikin ayyukan gwamnati.
Gwaman ya yi kira ga al’ummar jihar su zama masu haquri da yin addu’o’in alheri ga gwamnati. Ya ce, nan ba da dadewa ba za su ga ci gaba da kyakkyawan canji a rayuwa.
Kwamishinonin sun hada da Alhaji Abubakar Atiku Bunu da Alhaji Abubakar Ladan da Alhaji Ibrahim Bawa Kamba da Alhaji Ibrahim Muhammadu Augie da Alhaji Muhammadu Magawata Aliero da Alhaji Bala Sani Kangiwa da Alhaji Adamu Ibrahim Ngaske da kuma Hajiya Rakiya Janar Tanko Ayuba (mai ritaya), sai dai ba a fadi ma’aikatunsu ba.
Bayan kwamishinonin Gwamnan ya rantsar da masu ba shi shawara su uku da suka hada da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Aminu Musa Habibu Jega, sai Kyaftin din Mayaqan Ruwa Abubakar Zaki Mu’azu (mai ritaya) da Dokta Fati Mustapha Bunza.
Da yake mayar da jawabi a madadin sababbin kwamishinonin, Alhaji Abubakar Atiku Bunu, ya gode wa Gwamnan da al’ummar jihar bisa ba su wannan dama don su ba da tasu gudunmawa ga ci gaban jihar. Ya tabbatar wa Gwamnan cewa ba za su yi qasa a gwiwa ba wajen aiwatar da manufofin inganta rayuwar jama’ar jihar na gwamnatinsa ba.