An rantsar da sababbin shugabannin kungiyar direbobin tirela na Abbatuwa
kungiyar direbobi ta Jihar Legas ta rantsar da sababbin shugabannin kungiyar direbobin manyan motoci, reshen kasuwar Abbatuwa ta yankin Oko-Oba da ke karamar Hukumar Agege.Yayin bikin, wanda aka gudanar a sakatariyar kungiyar, a karshen makon da ya gabata, shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Tajudeen Agbege ya yi kiran mambobi su hada kai don ciyar da […]
kungiyar direbobi ta Jihar Legas ta rantsar da sababbin shugabannin kungiyar direbobin manyan motoci, reshen kasuwar Abbatuwa ta yankin Oko-Oba da ke karamar Hukumar Agege.
Yayin bikin, wanda aka gudanar a sakatariyar kungiyar, a karshen makon da ya gabata, shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Tajudeen Agbege ya yi kiran mambobi su hada kai don ciyar da kungiyar gaba.
Ya nuna muhimmancin sasanta tsakani, wanda ya fi zabe, saboda haka ya yi kira ga sababbin shugabbanin su zama tsintsiya-madaurinki daya, su tunkude bambanci tsakanin ’ya’yan kungiyar.
Da yake yi karin bayani, sabon shugaban kungiyar, Alhaj Muhammadu Bello Yusif ya bayyana wa Aminiya farin cikinsa dangane da zaben. “Zan yi aiki kafada-da-kafada da sauran membobin kungiya, don a samar da shugabanci nagari a kore cin hanci da rashawa. Zan tunkari wannan matsala ba tare da nuna bambanci ba. Zan bullo da sabbabin tsare-tsare don ciyar da kungiya gaba. Zan bar kofarta a bude don karbar shawarwarin da suka dace tare da sanar da ’yan kungiya abubuwan da ake ciki”. Inji shi.
Wadanda aka rantsar sun hada da matimakin shugaba, Alhaji Abdulkadir Salihu da sakatare, Alhaji Usman Yunusa da sakataren tsare-tsare, Alhaji Adamu A. A. Baba da Kodineta, Alhaji Ali Mai gidan wanka da ma’aji, Alhaji Ali danfulani da amintaccen kungiyar na daya, Malam danlami Nguru da kuma na biyu, Malam Bala Musa.