An rantsar da sabbin kwamishinoni 19 a Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda 19 da za su kula da harkokin ma’aikatun gwamnatin Jihar. Nadin nasu ya biyo bayan tsawon lokaci da gwamnatin jihar ta dauka ba tare da nada wani kwamishina ba tun bayan da Gwamnan ya sauke kwamishinoni 16 da ya fara nadawa a jihar […]

Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda 19 da za su kula da harkokin ma’aikatun gwamnatin Jihar.
Nadin nasu ya biyo bayan tsawon lokaci da gwamnatin jihar ta dauka ba tare da nada wani kwamishina ba tun bayan da Gwamnan ya sauke kwamishinoni 16 da ya fara nadawa a jihar kuma wannan nadi na nuni da cewa gwamnan ya kara yawan ma’aikatun jihar daga 16 zuwa guda 20.
Da yake rantsar da kwamishinonin a lokacin wani gagarumin biki da aka yi zauren taro na Multi Purpose da ke Bauchi, Gwamna Abubakar ya ce an zabo su ne bisa lura da aka yi da kwarewarsu da gogewarsu da cancantarsu. Ya bukace su da su dauki al’ummar Jihar Bauchi ba ki daya nasu ne, ta hanyar yi masu ayyukan da za su kawo ci gaba cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna bambanci kowane iri ba.
Gwamnan ya yi gargadin cewa ba zai yi wata-wata ba wajen korar duk wanda aka same shi da laifi a cikinsu saboda an kira su su yi aiki ne ba wai su bata aiki ba.
Daga cikin wadanda aka rantsar din sun hada da Ado Sarkin Aska Ma’aikatar kula da harkokin addinai, Rifkatu Samson Danna, muhalli, Rukayya Ibrahim Kewa, Ma’aikatar Mata, Haruna Deke Mohammed, Shari’a, Umar Ibrahim Sade, Watsa Labarai, Pharmacist Ibrahim Madaki Sale, Matasa da Wasanni, Barrister Yakubu Kirfi, Gona, Mohammed Mahmud Abubakar, Raya Karkara, Nasiru Babaginda Giade, kungiyoyi, Muhammadu Sani Bashir, Lantarki da fasaha, Umar Ibrahim Mohammed, Filaye da safiyo, Umar Abubakar Kazale, Masana’antu, Garba Sarki Akuyam, Maaikatar kudi.
Sauran su ne Nasirudeen Mohammed, kananan hukumomi, Dokta Zuwaira Ibrahim, Lafiya, Ibrahim Ayuba Suleiman, Ruwa, Farfesa Haruna danwanka, Ilimi, Musa Kaila Baima, Ma’adinai, yayin da mataimakin Gwamnan Jihar Injiniya Nuhu Gidado zai kula da Ma’aikatar ayyuka da sufuri.