An rantsar da sabon Babban Joji a Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar da Mai shari’a Musa danladi Abubukar a matsayin sabon Babban Jojin jihar, a ranar Talata da ta gabata. Da yake rantsar da shi, Gwamna Masari ya tabbatar masa cewa gwamnatinsa ba za ta sa baki ta kowace fuska domin yin katsalanda a  harkokin shari’a a jihar […]

An rantsar da sabon Babban Joji a Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar da Mai shari’a Musa danladi Abubukar a matsayin sabon Babban Jojin jihar, a ranar Talata da ta gabata.

Da yake rantsar da shi, Gwamna Masari ya tabbatar masa cewa gwamnatinsa ba za ta sa baki ta kowace fuska domin yin katsalanda a  harkokin shari’a a jihar ba. Kuma ya dara da cewa gwamnatinsa za ta ba fannin shari’a duk wata gudunmawa tare da hadin kai domin ganin cewa sashen shari’a ya gudanar da aikinsa ta fuskar aiwatar da adalci. Daga nan sai ya ja hankalin sabon Babban Jojin a kan ya yi dodarin ride kambin da jihar take da shi ta fuskar shari’a a dasar nan. 

 A jawabinsa, sabon Babban Jojin, ya tabbatar wa jama’a cewa zai yi iya dodarinsa na ganin ya sauke wannan nauyi da Allah Ya dora masa. Sannan ya ce jama’a za su samu biyan budatarsu ta fuskar shari’a, wadda budatar ita ce ta yin adalci a wajen aiwatar da shari’a.

Bikin rantsuwar ya gudanane a dakin taro na gidan gwamnatin jihar, a gaban jama’a. An kuma rantsar da sabon Babban Jojin ne domin maye gurbin Mai Shari’a Abdullahi Yusuf dafur saboda darewar wa’adin lokacin aikinsa.

An haifi Mai shari’a Musa danladi Abubukar a daramar Hukumar Funtuwa a ranar 21 ga Nuwamba 1958. Ya fara aikin shari’a a 1982 a Ma’aikatar Shari’a ta tsohuwar Jihar Kaduna.