An rantsar da sabon Gwamnan Ekiti Fayemi

An rantsar da zababben Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi yayin da za a ci gaba binciken tsohon gwamnan jihar, Ayo Fayose. Sabon Gwamnan dai tsohon Minista ne a ma’aikatar ma’adanai  kuma tsohon Gwamnan jihar wanda a yanzu ya dawo karo na biyu da nufin sake inganta harkokin jihar. Fayemi ya ce, Gwamnati mai barin gado […]

An rantsar da sabon Gwamnan Ekiti Fayemi

An rantsar da zababben Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi yayin da za a ci gaba binciken tsohon gwamnan jihar, Ayo Fayose.

Sabon Gwamnan dai tsohon Minista ne a ma’aikatar ma’adanai  kuma tsohon Gwamnan jihar wanda a yanzu ya dawo karo na biyu da nufin sake inganta harkokin jihar.

Fayemi ya ce, Gwamnati mai barin gado ta karbo bashin naira biliyan 170 don aiwatar da wasu ayyuka amma basu aiwatar da komai ba, wannan ba zai hana gwamnatin yanzu ci gaba da gudanar da ayyukan romon dimokaradiyya.