An rantsar da Sabon Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A shekaranjiya Laraba ne aka rantsar da sabon Shugaban kasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda zababben shugaban ya yi alkawarin tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin kasar.  Sabon Shugaban Faustin-Archange Touadera ya yi fatan ganin yana mutunta kundin tsarin mulki da tafiyar da harkokin kasar ba tare da nuna wani bambanci ba. Mista […]

An rantsar da Sabon Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
An rantsar da Sabon Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A shekaranjiya Laraba ne aka rantsar da sabon Shugaban kasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda zababben shugaban ya yi alkawarin tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin kasar.  
Sabon Shugaban Faustin-Archange Touadera ya yi fatan ganin yana mutunta kundin tsarin mulki da tafiyar da harkokin kasar ba tare da nuna wani bambanci ba. Mista Touadera tsohon firaiministan kasar ne kuma farfesa kan fannin lissafi.
An yi bikin rantsuwar ne a filin wasanni da ke birnin Bangui, inda shugabannin kasashen duniya da wakilai dama suka halarta.
Cikin shugabannin da suka halarta akwai Shugaban Guinea Teodoro Obiang Nguema, da Shugaban Guinea Denis Sassou Nguesso da Ministocin tsaro na Faransa da takwaransa na Harkokin kasashen Waje.
Har ila yau, a shekaranjiya Laraba ne kasar Faransa take kwashe sojojinta daga kasar,  bayan kwashe shekaru kusan uku suna aikin wanzar da zaman lafiya.
Tun dai lokacin da ‘yan tawaye suka tumbuke shugaban kasar Francoise Bozize a shekarar 2013, kasar take fama da rikicin kabilanci da na addini, al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da kuma jikkita dubai.