An rantsar da Sakataren Gwamnatin Kebbi da kantomomin kananan hukumomi

An rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Baballe Umar Yauri da kantomomin kananan hukumomi 20 daga cikin 21 da ke jihar.Rantsuwar ta biyo bayar amincewa da nadinsu da majalisar jihar tayi, bayan rushe shugabanin kananan hukumomin a kwanaki bayan cikar wa’adin mulkinsu.Rantsuwar wadda Mai shari’a Faruk Hassan Bunza ya ba su a madadin […]

An rantsar da Sakataren Gwamnatin Kebbi da kantomomin kananan hukumomi
An rantsar da Sakataren Gwamnatin Kebbi da kantomomin kananan hukumomi

An rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Baballe Umar Yauri da kantomomin kananan hukumomi 20 daga cikin 21 da ke jihar.
Rantsuwar ta biyo bayar amincewa da nadinsu da majalisar jihar tayi, bayan rushe shugabanin kananan hukumomin a kwanaki bayan cikar wa’adin mulkinsu.
Rantsuwar wadda Mai shari’a Faruk Hassan Bunza ya ba su a madadin Babban Jojin Jihar Mai shari’a Bala Mairiga ta gudana ne a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya umurci kantomomin kananan hukumomin su inganta rayuwar al’ummar yankunansu musamman matasa kuma su bai wa sarakuna goyon bayan da ya kamata.
Gwamnan ya ce kada wani kantoma ya ce zai kori wani ma’aikaci haka nan ba tare da wadanda suke da alhakin korar ma’aikaci idan ya yi laifin da za a kore shi sun yanke hukuncin haka ba, kuma ya ce su ba da goyon baya ga shugabannin Jam’iyyar APC a yankunansu kuma su rika yin shawara da su, domin ci gaban yankunan da jihar baki daya.
Da ya juya kan Sakataren Gwamnatin Jihar, Gwamnan ya ce kwarewarsa a aiki da sanin ya kamata, ya sa majalisa ta amince a ba shi mukamin domin ya dora daga inda ya tsaya lokacin yana Shugaban Ma’aikatan Jihar.
Gwamnan ya yi alkawarin gyara hanyar Jega zuwa Yawuri da kuma inganta ba da ruwan sha a garin Yawuri.